Friday, March 6, 2009

Budaddiyar Wasika Zuwa ga Shekarau:

Budaddiyar Wasika Zuwa ga Shekarau:
Martani ga ‘yan Jagaliyar Daraktocin gwamnatin kano
Daga
Comrade Rabi’u Na’auwa Balarabe


Ya maigirma Gwamana, na zabi rubuta maka wannan zasika ne saboda yanda na ga yan jagaliyar siyasa suna neman kutso kai cikin al’amuranka, ta hanyar wasu daraktocinka dake faman tabka barna ga al’umar dake karkashinka ta jihar kano ,sannan kokarin kar ka gane abinda suke aikatawa ya sa suke yaki da duk wanda ya dauri niyyar gayamaka gaskiya, wannan yasa suka fara dauko yan jagaliyarsu suna tsara musu wasika su kuma su saka sunayensu su turo maka duk wai a kokrinsu na kar ka gane barnar da suke tabkawa.
Ya maigirma gwamna idan zaka yi la’akari da wata wasika wadda wani mai suna Aminu M Aminu ya rubuto maka wadda aka buga a jaridar Ledership Hausa ta 20 ga watan fabarairu 2009, mai dauke da tsabar banbadanci irin na yan jagaliyar siyasa masu ingiza mai kantu ruwa, wadda nasan in har za’ayi la’akari da kwarewarka ta tsohon malamin ilmi ba zaka taba kula waccan wasika ba, domin nasan tuni za ka yi mata masauki a kwandon shara
Ranka ya dade lokaci ya yi da yakamata ka fahimci irin bakin jini da dumbin zagin da wasu daga cikin daraktocinka suke janyo maka daga miliyoyin al’ummarka ta jihar kano. Nasan baka da masaniya a kan hakan, face irinsu sheme da suke kokarin fayyace maka halin da ake ciki.
Ranka shi dade shi kanshi sheme ina da tabbacin bai futo ya gayamaka gabadayan abinda ke faruwa ba sai dai kawai ya yi kokarin sanar da kai wasu daga cikin abinda ke faruwa.
Ranka shi dade sau da yawa mutane irinsu Abubakar Rabo suna bada muhimmiyar gudummawa wajan kashe jiharka ta kano, ta yanda har mutane suka fara zargin gwamnatinka da wasa da hankalin mutane tare da juyar da hankalinsu bisa kame ‘yan fim, tare da jefasu cikin halin kaka nikayi, gefe guda kuma daraktocin naka suna tabka al’mundahana a kokarinsu na kashe jaharka ta kano.
Ranka ya dade ire-iren wadannan matsaloli ne suka sa masu yiwa gwanatinka kallon Adalar gwamnati, ya juye zuwa azzaluma.
Ya maigirma gwamna kokarin rufa-rufa da wasu daraktocinka suke yi maka shi ne yasa suka fara turo da yan jagaliyarsu, suna kokarin cin mutuncin duk mai kokarin gayamaka gaskiya, ina mamakin yanda Malam Aminu ya yi ta soki burutsu a kokarinsa na son ya kare Rabo da hukumarsa kamar yanda ya ce:
Saudayawa mutane irinsu Ibrahim Sheme suna cewa wai ana fakewa ne da shari’a ko addini amma ba za’a iya kawo hujja ba.
Kodayake bansan wace irin shaida malam Aminu yake bukata ba, amma da sai in ce na yi matukar mamaki da wannan Magana ta futo daga bakin dan jihar kano, musamman don ganin duk wata hujja a bayyane take, idan aka yi la’akari da yanda ‘yan jihar kano ke maganganu ko kallon gwamnatin jihar kano a matsayin wadda shari’arta ta kare a kan yan fim, gefe guda kuma, ga daruruwan gidajen karuwai,caca, da gidajen yada fasadi, tare da dubban gidajen giya, da na holewar manyan mutane da matasa wadanda suke birjik a cikin jihar kano suna cin karensu babu babbaka, ta yanda in har zaka shiga wasu wurare da daddare sai ka rantse a wasu wuraren shakatawa kake a kasashen turai, amma gwamanatin kano ta yi biris da wannan ta fake da kama yan fim tana daurewa a matsayin gwamnatin musulunci.
Sai kuma inda malam Aminu yake cewa; Ya yi mamakin shaguben da sheme yake yi na cewa wai babu kotun hukunta ‘yan luwadi da karuwai da ‘yan caca a jihar kano. Domin fadar hakan ko dai tsantsar jahilci ne, ko kuma son zuciya. Wai Idan har sheme bai sani ba duk wadannan akwai kotunansu sune kotun shari’ar musulunci.
Wannan Magana ta Aminu sai ta bani dariya musamman yanda ya bankado zahirin Magana ya futo da ita fili, mararan ya nuna yanda gwamnatin jihar kano ta kare shari’ar musuluncinta a bangare daya, ko kuma ta zama yaudara, a nan Aminu yana Magana akan cewa kotunan shari’ar musulunci dake cikin jihar kano sun kunshi duk wani laifi da ake aikatawa a jihar amma banda ‘yan fim tinda a bayyane yake yan fim suna da kotu Tasu ta kansu, wadda gwamnatin jihar kano ta ware musu. To abin tambaya anan shi ne wannan yana nufin gwamnatin jihar kano bata yarda da kotunan shari’ar musulunci dake cikin kano ba, ko kuwa bata gamsu da yanda suke yanke hukunci bane shi yasa idan ta kama yan fim da laifi bata kaisu can don yanke musu hukunci? Wannan abin tambaya ne, tinda gashi an ware musu kotu tasu ta daban wadda ba ta musulunci ba, bayan kuma suma musulmi ne kamar kowa, in kuwa haka ne mene ne dalililin gwamnatin jihar kano na yiwa kotunan shari’ar musulunci kishiya tinda ana ikirarin gwamnatin jihar kano gwamnatin musulunci ce, sannan duk duniya babu wata gwamnatin musulunci da ta yiwa kotunan shari’ar musulunci kishiya sai jihar kano, wadda ta kirkiri Mobile Cort domin hukunta ‘yan fim da marubuta, bayan kuma su ba kafirai ba, musulmi ne ‘ya’yan musulmi jikokin musulmi, kai har ma hafizan Alkur’ani akwai a cikin su, ko kuwa dukkaninsu gwamnatin jihar kano ta mayar dasu kafirai da ta ware musu kotun musamman ta futar dasu daga hurumin kotunan musulunci?
Sai kuma batunka na cewa wai Tsantsar son zuciya ne yasa sheme ya ce wai yaki da gwamnatin jihar kano ke yi da finafinai ya haifar da rashin aikin yi
A nan ni abinda zan ce lallai ka cika tsantsar maras kishin jihar kano, ko kuma ince kasa baki daya.
Shin ko malam Aminu yasan adadin mutanen dake cin abinci ta hanyar FiM ? kama daga kan masu Printing,Camera,Editing,da kuma yan kasuwa masu siyar da kaset diloli da masu kokarin tasowa, da kuma dubban su kansu ‘yan fim din da iyalansu, wadanda mafi yawansu yanzu sun zama marasa aikin yi da masu zaman banza. Shin ko malam Aminu ya san mutum nawa suka zama yan maula a sanadiyyar haka ? Allah kadai ya san adadin mutanen da a sanadiayar haka suka shiga masifar bashi da cuwa-cuwa da zaman banza a jihar kano.
Sai wata magana da tasa mini shakkun in har Aminu ya san abinda yake fada, ba don komai ba sai don yanda yake tubka sannan ya dawo ya warware abunsa kamar yanda ya ce :
Kokarin da Rabo yake yi bisa harkar fim shi ne yasa har jama’ar jihar kano suke samun nutsuwar da gaske gwamnati take yi wajan shar’ar musulunci a jihar kano
To a nan kaga maganar da ka karyata a baya ta cewa shari’ar gwamnatin jihar kano ta kare ne a kan ‘yan fim ita ce ka dawo ka tabbatar da ita da bakinka. In kuwa kamar yanda ka fada haka ne to lallai akwai zalunci ga kamun da ake yiwa ‘yan fim a jihar kano, sabo da an bar jaki ne kuma an koma ana dukan taiki, tinda an ce shari’ar musulunci ake a kan yan fim amma kuma in an kamasu ba’a kaisu kotun shari’ar musulunci. A zahiri wannan ba karamin zalunci bane.
Ya maigirma gwamna yakamata ka sani wakilinka da ka aje a hukumar tace finafinai da daba’i, ba wani aiki suka fi kwarewa akansa ba face cusa kiyayya da tsanarka a idanun miliyoyin al’umarka ta jihar kano.
Ranka shi dade ina mai kara jan hankalinka ga yan jagaliyar siyasa wadanda wasu daraktocinka ke yin hayarsu suna tsara musu wasiku na bogi wai ala dole sai ka yarda da zamba tare da kokarin kashe jiharka ta kano.
Ya maigirma gwamna ire-iren wadannan ne kake yaki da munanan dabi’unsu, kamar yanda nasan ka kafa hukumar Adaidaita Sahu domin cusa da’a a zukatan al’umma tare da yaki da munanan dabi’u, to ba wasu bane wannan hukuma take yaki dasu face ire-irensu masu bi kofar ofis-ofis suna banbadanci suna hana a yiwa talakawa aiki,sai dai a turasu su ci mutuncin wannan su zagi wancan.Ranka ya dade ganin hukumar Adaidaita sahu ta dage wajan yaki dasu ne yasa suka futo da wannan sabuwar hanyar ta a rubuta wasika a basu suci mutuncin al’umma.
Ya maigirma gwamna kamar yanda na jima da saninka a matsayin gwamna mai adalci ka yi duba da idon basira zuwa ga hukumar Rabo da irin barnar da yake faman tabkawa ga al’umma da kasa baki daya. Sannan ka amsa kukan ‘yan jiharka ta kano da suke neman agaji bisa uzzurawa yaransu da kannensu da mazajensu wadanda tuni Rabo ya mayar da wasunsu ‘yan maula masu zaman banza. Yakamata ka dawo da mutuncinka da na Jam’iyarka wanda tini wasu daraktocinka suka zubar maka.

No comments:

Post a Comment