Friday, March 6, 2009

Budaddiyar Wasika Zuwa ga Shekarau:

Budaddiyar Wasika Zuwa ga Shekarau:
Martani ga ‘yan Jagaliyar Daraktocin gwamnatin kano
Daga
Comrade Rabi’u Na’auwa Balarabe


Ya maigirma Gwamana, na zabi rubuta maka wannan zasika ne saboda yanda na ga yan jagaliyar siyasa suna neman kutso kai cikin al’amuranka, ta hanyar wasu daraktocinka dake faman tabka barna ga al’umar dake karkashinka ta jihar kano ,sannan kokarin kar ka gane abinda suke aikatawa ya sa suke yaki da duk wanda ya dauri niyyar gayamaka gaskiya, wannan yasa suka fara dauko yan jagaliyarsu suna tsara musu wasika su kuma su saka sunayensu su turo maka duk wai a kokrinsu na kar ka gane barnar da suke tabkawa.
Ya maigirma gwamna idan zaka yi la’akari da wata wasika wadda wani mai suna Aminu M Aminu ya rubuto maka wadda aka buga a jaridar Ledership Hausa ta 20 ga watan fabarairu 2009, mai dauke da tsabar banbadanci irin na yan jagaliyar siyasa masu ingiza mai kantu ruwa, wadda nasan in har za’ayi la’akari da kwarewarka ta tsohon malamin ilmi ba zaka taba kula waccan wasika ba, domin nasan tuni za ka yi mata masauki a kwandon shara
Ranka ya dade lokaci ya yi da yakamata ka fahimci irin bakin jini da dumbin zagin da wasu daga cikin daraktocinka suke janyo maka daga miliyoyin al’ummarka ta jihar kano. Nasan baka da masaniya a kan hakan, face irinsu sheme da suke kokarin fayyace maka halin da ake ciki.
Ranka shi dade shi kanshi sheme ina da tabbacin bai futo ya gayamaka gabadayan abinda ke faruwa ba sai dai kawai ya yi kokarin sanar da kai wasu daga cikin abinda ke faruwa.
Ranka shi dade sau da yawa mutane irinsu Abubakar Rabo suna bada muhimmiyar gudummawa wajan kashe jiharka ta kano, ta yanda har mutane suka fara zargin gwamnatinka da wasa da hankalin mutane tare da juyar da hankalinsu bisa kame ‘yan fim, tare da jefasu cikin halin kaka nikayi, gefe guda kuma daraktocin naka suna tabka al’mundahana a kokarinsu na kashe jaharka ta kano.
Ranka ya dade ire-iren wadannan matsaloli ne suka sa masu yiwa gwanatinka kallon Adalar gwamnati, ya juye zuwa azzaluma.
Ya maigirma gwamna kokarin rufa-rufa da wasu daraktocinka suke yi maka shi ne yasa suka fara turo da yan jagaliyarsu, suna kokarin cin mutuncin duk mai kokarin gayamaka gaskiya, ina mamakin yanda Malam Aminu ya yi ta soki burutsu a kokarinsa na son ya kare Rabo da hukumarsa kamar yanda ya ce:
Saudayawa mutane irinsu Ibrahim Sheme suna cewa wai ana fakewa ne da shari’a ko addini amma ba za’a iya kawo hujja ba.
Kodayake bansan wace irin shaida malam Aminu yake bukata ba, amma da sai in ce na yi matukar mamaki da wannan Magana ta futo daga bakin dan jihar kano, musamman don ganin duk wata hujja a bayyane take, idan aka yi la’akari da yanda ‘yan jihar kano ke maganganu ko kallon gwamnatin jihar kano a matsayin wadda shari’arta ta kare a kan yan fim, gefe guda kuma, ga daruruwan gidajen karuwai,caca, da gidajen yada fasadi, tare da dubban gidajen giya, da na holewar manyan mutane da matasa wadanda suke birjik a cikin jihar kano suna cin karensu babu babbaka, ta yanda in har zaka shiga wasu wurare da daddare sai ka rantse a wasu wuraren shakatawa kake a kasashen turai, amma gwamanatin kano ta yi biris da wannan ta fake da kama yan fim tana daurewa a matsayin gwamnatin musulunci.
Sai kuma inda malam Aminu yake cewa; Ya yi mamakin shaguben da sheme yake yi na cewa wai babu kotun hukunta ‘yan luwadi da karuwai da ‘yan caca a jihar kano. Domin fadar hakan ko dai tsantsar jahilci ne, ko kuma son zuciya. Wai Idan har sheme bai sani ba duk wadannan akwai kotunansu sune kotun shari’ar musulunci.
Wannan Magana ta Aminu sai ta bani dariya musamman yanda ya bankado zahirin Magana ya futo da ita fili, mararan ya nuna yanda gwamnatin jihar kano ta kare shari’ar musuluncinta a bangare daya, ko kuma ta zama yaudara, a nan Aminu yana Magana akan cewa kotunan shari’ar musulunci dake cikin jihar kano sun kunshi duk wani laifi da ake aikatawa a jihar amma banda ‘yan fim tinda a bayyane yake yan fim suna da kotu Tasu ta kansu, wadda gwamnatin jihar kano ta ware musu. To abin tambaya anan shi ne wannan yana nufin gwamnatin jihar kano bata yarda da kotunan shari’ar musulunci dake cikin kano ba, ko kuwa bata gamsu da yanda suke yanke hukunci bane shi yasa idan ta kama yan fim da laifi bata kaisu can don yanke musu hukunci? Wannan abin tambaya ne, tinda gashi an ware musu kotu tasu ta daban wadda ba ta musulunci ba, bayan kuma suma musulmi ne kamar kowa, in kuwa haka ne mene ne dalililin gwamnatin jihar kano na yiwa kotunan shari’ar musulunci kishiya tinda ana ikirarin gwamnatin jihar kano gwamnatin musulunci ce, sannan duk duniya babu wata gwamnatin musulunci da ta yiwa kotunan shari’ar musulunci kishiya sai jihar kano, wadda ta kirkiri Mobile Cort domin hukunta ‘yan fim da marubuta, bayan kuma su ba kafirai ba, musulmi ne ‘ya’yan musulmi jikokin musulmi, kai har ma hafizan Alkur’ani akwai a cikin su, ko kuwa dukkaninsu gwamnatin jihar kano ta mayar dasu kafirai da ta ware musu kotun musamman ta futar dasu daga hurumin kotunan musulunci?
Sai kuma batunka na cewa wai Tsantsar son zuciya ne yasa sheme ya ce wai yaki da gwamnatin jihar kano ke yi da finafinai ya haifar da rashin aikin yi
A nan ni abinda zan ce lallai ka cika tsantsar maras kishin jihar kano, ko kuma ince kasa baki daya.
Shin ko malam Aminu yasan adadin mutanen dake cin abinci ta hanyar FiM ? kama daga kan masu Printing,Camera,Editing,da kuma yan kasuwa masu siyar da kaset diloli da masu kokarin tasowa, da kuma dubban su kansu ‘yan fim din da iyalansu, wadanda mafi yawansu yanzu sun zama marasa aikin yi da masu zaman banza. Shin ko malam Aminu ya san mutum nawa suka zama yan maula a sanadiyyar haka ? Allah kadai ya san adadin mutanen da a sanadiayar haka suka shiga masifar bashi da cuwa-cuwa da zaman banza a jihar kano.
Sai wata magana da tasa mini shakkun in har Aminu ya san abinda yake fada, ba don komai ba sai don yanda yake tubka sannan ya dawo ya warware abunsa kamar yanda ya ce :
Kokarin da Rabo yake yi bisa harkar fim shi ne yasa har jama’ar jihar kano suke samun nutsuwar da gaske gwamnati take yi wajan shar’ar musulunci a jihar kano
To a nan kaga maganar da ka karyata a baya ta cewa shari’ar gwamnatin jihar kano ta kare ne a kan ‘yan fim ita ce ka dawo ka tabbatar da ita da bakinka. In kuwa kamar yanda ka fada haka ne to lallai akwai zalunci ga kamun da ake yiwa ‘yan fim a jihar kano, sabo da an bar jaki ne kuma an koma ana dukan taiki, tinda an ce shari’ar musulunci ake a kan yan fim amma kuma in an kamasu ba’a kaisu kotun shari’ar musulunci. A zahiri wannan ba karamin zalunci bane.
Ya maigirma gwamna yakamata ka sani wakilinka da ka aje a hukumar tace finafinai da daba’i, ba wani aiki suka fi kwarewa akansa ba face cusa kiyayya da tsanarka a idanun miliyoyin al’umarka ta jihar kano.
Ranka shi dade ina mai kara jan hankalinka ga yan jagaliyar siyasa wadanda wasu daraktocinka ke yin hayarsu suna tsara musu wasiku na bogi wai ala dole sai ka yarda da zamba tare da kokarin kashe jiharka ta kano.
Ya maigirma gwamna ire-iren wadannan ne kake yaki da munanan dabi’unsu, kamar yanda nasan ka kafa hukumar Adaidaita Sahu domin cusa da’a a zukatan al’umma tare da yaki da munanan dabi’u, to ba wasu bane wannan hukuma take yaki dasu face ire-irensu masu bi kofar ofis-ofis suna banbadanci suna hana a yiwa talakawa aiki,sai dai a turasu su ci mutuncin wannan su zagi wancan.Ranka ya dade ganin hukumar Adaidaita sahu ta dage wajan yaki dasu ne yasa suka futo da wannan sabuwar hanyar ta a rubuta wasika a basu suci mutuncin al’umma.
Ya maigirma gwamna kamar yanda na jima da saninka a matsayin gwamna mai adalci ka yi duba da idon basira zuwa ga hukumar Rabo da irin barnar da yake faman tabkawa ga al’umma da kasa baki daya. Sannan ka amsa kukan ‘yan jiharka ta kano da suke neman agaji bisa uzzurawa yaransu da kannensu da mazajensu wadanda tuni Rabo ya mayar da wasunsu ‘yan maula masu zaman banza. Yakamata ka dawo da mutuncinka da na Jam’iyarka wanda tini wasu daraktocinka suka zubar maka.

Sunday, January 25, 2009

ASALIN HAUSAWA DA RUBUTUN HAUSA NA AINAHI


ASALIN HAUSAWA DA RUBUTUN HAUSA NA AINAHI
DAGA
DOKTA KORAO H. MAHAMADU











LAkCAR DA AKA GABATAR A ƘARƘASHIN
INUWAR KWAMITIN ƘASA (NAJERIYA)
KAN NAZARIN HARUFFAN HAUSA









WURI: BABBAN DAKIN TARO
JAMI’AR JAHAR KADUNA, KADUNA

RANA: LITINI, 24 GA YULI, 2006

LOKACI: 10:00 NA SAFE



ABIN DA KE CIKI

GABATARWA……………………………………………………………………………………… ………….2
I./. HaRshen hausa. 3
1.1./.Da kalmar RA. 4
1.2./. Da kalmar RE. 4
1.3./. SAKAMAKO.. 5
1.3.1./. SAKAMAKO KAN HARSHE. 5
1.3.2./. SAKAMAKO KAN TARIHI 6
II./.RUBUTU. 8
2.1. ALAMAR RUBUTUN FARKO.. 8
2.1.1/. RUBUTU SUMER. 8
2.1.2./. RUBUTU MAI LUNGU KO CUNEIFORME. 9
2.1.3./. RUBUTU NA HIEROGLYPHE. 10
2.2./. ALAMAR BABBAƘUN DUNIYA. 10
2.2.1./. BABBAKUN FARAR FATA. 10
2.2.2./. MA’ANAR BABBAƘUN A GIMILCE. 12
2.2.3./. BABBAƘUN BAƘAR FATA. 15
III./. A SAKE BINCIKE KAN RUBUTUN AINAHI 16
3.1./.AINAHI KO TUSHEN RUBUTUN HAUSA. 16
3..2./. ANFANINSA. 16
3..3./. ALAMAR RUBUTUN HAUSA. 16
3.4./. YANAYIN FURUCIN HAUSA. 16
3.5./. BABBAƘUN HAUSA. 16
3.5.1./. WASULLAN HAUSA. 17
3.5.2./. LANGAYEN WASULLAI 17
3.5.3../. GOYON WASULLAI 17
3.5.4./.AYOYI 17
3.5.5./. ƴAN LISSAFI 17
3.5.6./. WAKILLAN ƴAN LISSAFI 17
TAƘAITAWA. 18

RATAYE…………………………………………………………………………………………17

LITTATTAFAN BINCIKE……………………………………………………………………….17


AINAHIN HAUSA


GABATARWA

A’uzu billahi minal shaitani razim. Bismillahi Rahamani Rahim
Assalamu alaikum jama’a Yan uwa, kuma barkammu da yau.

Idan ba ku manta ba, yau da ‘yan shekaru ke nan, muka ce muku, harshen hausa, harshe ne na farko, wanda daga gare shi ne yawancin harsunan duniyar nan suka fita; kuma mun ƙara da cewa hausa na da rubutu, wanda shi ma ya aifi yawancin rubutu da yawancin mutane ke anfani da shi kamar su Latina, Larabci da sauransu. To, ina hujjar wannan bayani?

Za mu yi anfani da harshe da rubutun hausa, domin a gane. Sai ku biyo mu sau da ƙafa.

I. /. Harshen hausa

Tabbat, harshen hausa, harshen farko ne, kuma da izinin Allah, za mu gwada muku hujjojin. Yanzu dai za mu yi anfani kaɗan da harshen hausa don mu nuna muku kaɗan daga cikin martabobinsa.

Idan ba ku manta ba, ƙasa da rana da wata da tarmamu da saurensu, sun bayyana ne a gare mu, bayan tsayuwar jirgin tsira na Annabi Nuhu (T.A.A.T.G). A lokacin da rana da wata da tarmamu suka bayyana, wata ƙabila ta riƙa bauta musu, bauta ta fuskar addini. Kuma jagoran addinin shi ne wakilin rana da wata da tarmamu da saurensu.

To wace ƙabila ce ta farko wadda ta bauta ma waɗannan abubuwan? Ai babu shakka HAUSAWA ne !

Hujja ?

Sunaye da kalmomi kuma da karin magana dangane da rana da wata da tarmamu da saurensu da ake samu a cikin harshen hausa. Wakillan Rana da Dare, can da farko, RA da RE ake kiransu da hausar ainahi.

Ƙaƙa RA da RE za su ba mu kalmomi da sunaye da karin magana da yawa a cikin harshen hausa ?

RA da RE wakillan rana da dare ne, kuma su ne za su yaɗaɗa addini ko’ina cikin duniyar nan. Yaɗuwar addinin RA da RE (kowa da nashi), zai ƙarfafa harshen hausa ta fuskar kalmomi da sunaye da karin magana, kamar haka:
1.1. /. Da kalmar RA.
Za mu samu haka:
- RA - NAWA
- RA - NAW
- RA – NA

RANAWA, da RANAW da RANA, dukkansu ma’anarsu guda ce, cewa da ALLAH NE. To, masu sauraren mu, kar a zarge mu da cewa mun soki ra’ayin addinin musulunci ko na christa ko kuma can wani addini, muna bada wannan sanarwa, domin a san mafari da manufa. A game da wannan lamari na RA - NA, waɗanne kalmomi ne da sunaye da karin magana za mu samu?
A kwai :
- RANA
- RANI
- RANAU
- RAKEA
- RANARKA
- BA KA DA RANA
- RANKA YA DAƊE
- ds…

Idan an ji kuma an gane da yanda muka samu kalmomi da sunaye da karin magana da RA ko da RE, ƙaƙa ne? Wannan tambayar ce ke ba mu damar anfani da aji na biyu, cewa da RE.

1.2. /. DA KALMAR RE

A fuskar bauta ma rana da wata da tarmamu, ba a kiran RA ba tare da RE ba. Wannan al’amarin zai ba mu kalmomi, da sunaye da Karin magana kamar haka:
- RA – NAWA da RE
- RA – NAW da RE
- RA – NA da RE

Dukan waɗannan sheɗarun ma’anarsu guda ce, cewa da RANA DARE, inda muke ƙwanƙwance sunayen rana da dare, wa’anda suke makamman ainahi na awon lokaci ga harshen hausa. A game da RE waɗanne kalmomi da sunaye da Karin magana ne za mu samu?
A kwai:
- DARE
- ADARE
- BABARBARE
- BA’ADARE
- BA’ARE
- GARE KA
- RENI
- ds...
Kun dai ji a taƙaice, kuma kun gane da yanda muka samu kalmomi da sunaye da karin magana da waɗannan kalmomin cewa da RA da RE, waɗanda a duniyar nan, ba su da ma’ana in ba ga harshen hausa ba. Kuma idan ba ku yarda ba ku jarraba da duk harshen da kuke so, ku gani!
1.3. /. SAKAMAKO

Dangane da wannan sanarwa, mine ne ya kamata a gane kuma a riƙe?

Na ɗaya shi ne, yanda harshen hausa ke gudanar da al’amuransa.
Na biyu ko, ya shafi kaɗan daga cikin tarihin hausawa.
Sai ku biyo mu sau da ƙafa.
1.3.1. /. SAKAMAKO KAN HARSHE

Abin da ya kamata a gane na farko a game da harshen hausa shi ne, harshen hausa kamar ƙwame yake, ba harshe ba ne wanda ke buɗe kamar yawancin harsunan duniya;

Abu na biyu wanda ya kamata a gane, kuma a riƙe game da harshen hausa shi ne wannan haɗuwa, gamuwa, ɗoriya, ko kuma auren ƙaramin baƙi da babban baƙi, wanda ake kira gaɓa ko syllable a turance. Harshen hausa ne kaɗai zai bada fassara da ma’ana a kowace gaɓa;

Abu na ukku wanda ya kamata a gane shi ne lauɗi: ana iya a ja shi, ko a taƙure shi, ko kuma a lanƙwasa shi; wannan lauɗin na harshen hausa, ya ɗauko tushensa ne daga wannan ɗoriyar gaɓoɓin.

Wannan lauɗin na harshen hausa na ba mu damar kwatamta sheɗara ko jumla, kamar sarƙa, ita kuma gaɓa ko syllable kamar zobe. Ku san da sani cewa, idan a kwai zobe, to sarƙa ba ta ƙarewa, haka harshen hausa yake;

Abu na huɗu wanda ya kamata a gane ga harshen hausa shi ne: duka kalma, sheɗara ce ko jumla; haka kuma duka sheɗara ko jumla na iya taƙurewa ta koma kalma, kamar dai yanda kuka ji ɗazu.

Abu na biyar wanda ya kamata a riƙe shi ne bambanci da ke da kwai tsakanin harsunan duniya:

- Akwai harsuna na ainahi, kamar harshen hausa; Harshen ainahi kamar ƙwame yake, ba harshe ba ne wanda ke buɗe, a rufe yake, idan babu mabuɗi, sai a yi haƙuri.
- A kwai aifaffi; Su dai aifaffin harsuna, rabi rufe rabi buɗe; kuma ba su kama da ƙwame.
- A kwai yayayyi, waɗanda a buɗe suke samsamsam.

Abin da ya kamata a gane kuma a riƙe a nan shi ne, kwatamci da harshen hausa; duk harshen da ba ya yi kamar harshen hausa, to ba na ainahi ne ba, kuma ƙarshensa ɓacewa, ba yin mutum ba ne, sarautar Allah ce.

Kun dai ji a taƙaice kaɗan daga cikin al’amuran harshen hausa, yanzu sai mu shiga kaɗan daga cikin tarihin hausawa.

1.3.2./. SAKAMAKO KAN TARIHI

Sakamako na farko kan tarihi, shi ne tabbata muku da cewa, mutanen farko a duniyar nan, wanda suka fara addini, baƙaƙe ne, kuma hausawa ne; sun fara da addinin rana da wata da tarmamu, sai addinin gumaka ya biyo, sannan sauran;

Sakamako na biyu kan tarihi shi ne, maimaitawa da ƙwanƙwancewa bisa ga mutanen farko na ƙasar Misira ko Egypte.

Idan ba ku manta ba, Farfesa CHEICK ANTA DIOP (Allah ya jiƙan shi, amin) na ƙasar Sanagal, ya tabbata muna da cewa mutanen farko na ƙasar Misira, ainahi baƙaƙe ne, mu kuma muka ƙara da cewa hausawa ne. Ga hujjojin:

- Hujja ta ɗaya, hoto ne, da muka ɗauko cikin littafinsa mai suna baƙaƙe da al’adunsu, ko kuma NATIONS NEGRES ET CULTURES, bugu na huɗu, shafi na ɗari da goma. Shi dai wannan hoto an ɗauke shi ne kamar Fira’auna; Fira’auna ko kun san Misisra ce;
- Hujja ta biyu, ita ce MAGAJIYA RAKEA, wadda ke ta ukku cikin sarakunan Gobirawa, sanannu. Za mu ɗan dakatawa kaɗan bisa ga MAGAJIYA RAKEA domin ƙarin bayani.

Magajiya, kun san dai sarautar mata ce a ƙasashemmu na hausa? Kuma wakiliyar ‘yan bori ce!
Rakea ko suna ne na mata a ƙasashemmu na hausa.

Idan ba ku manta ba, mun shaida muku da cewa, harshen hausa, harshe ne mai kwaɗo, to za mu sa mabuɗi mu buɗe kwaɗon domin mu gane ma’anar wannan suna na RAKEA.

RAKEA suna ne mai nuhin RA-KE-A-EA. Kun gani a nan, sheɗara ce, ko jumla. Idan ta taƙure, ta koma suna, sai ta ba mu RAKEA.

EA, INNA dukansu ma’anarsu guda ce, cewa da uwar ‘yan bori.

A taƙaice RAKEA na nuhin uwar ‘yan bori. Wato MAGAJIYA.

Wannan maccen, cewa da MAGAJIYA RAKEA, ita ce gimbiya ta farko a duniyar nan, wadda ta kafa iko da addini a cikin ƙasar Misira.

- Hujja ta ukku, wannan sunan na Fira’auna, ko kuma FARAON, wanda ‘yan mulkin mallaka suka laƙa ma sarakunan Misira, kalmar hausa ce, kuma tana dangane da wannan gimbiyar, bahausa, cewa da RAKEA.

Abin ganewa a nan, shi ne can da ainahi FARAU a ke cewa; kuma FARAU na nuhin waɗanda suka fara kafa mulki da addini a cikin ƙasar ta Misira, da magadansu; idan kun yi la’akari, dukansu na da sunaye wanɗanda ake kiran su da shi.

Kenan al’amarin Fira’auna daga baya ne ya wanzu, zamanin ikon ‘yan mulkin malakka, inda suke kiran Sarkin Misira da wannan laƙabin.

- Hujja ta huɗu, rijiya ukku cikin ƙasa ukku; ko wace rijiya na game da ‘yar uwarta da sarƙa; rijiya ta farko na nan cikin Misira; biyu ɗin na nan cikin ƙasashen Afirka, baƙar fata.
- Sakamako na ukku kan tarihi shi ne gadon iko da addini na gargajiya gare mu hausawa.

Iko da addini na gargajiya, sun ɗauko tushensu ne daga RA da RE; kuma wannan kalma ce hujja: HATTARASA. Wanda duk ya je fadar sarakunammu na gargajiya ya ji wannan kalma; to minene ma’anar wannan kalmar? Za mu sa mabuɗi mu buɗe kalmar domin mu gane ma’ana ; sai ku biyo mu sau da ƙafa:

HATTARASA
HAR TA RA SA
HAL TA RA SA
HAG GA SARAUTA RA SA
HAR GA SARAUTA RA SA
HAL GA SARAUTAR RA SA
HATTARA SA!
Dukkan su ma’anarsu guda ce, cewa da hattarasa.

Kuma duka sarki na hausa da rawani aka san shi ; kenan rawani hikimar sarauta ce ; idan haka gaskiya ne to mine ne ma’anar rawani? A nan ma za mu yi anfani da mabuɗi domin fahimta ;
RAWANI kalma ce wadda ta ƙumshi gaɓa ukku :

A kwai RA (ku tuna da bayanin ɗazu),
a kwai WA (mai nuhin babba, magaji),
a kwai NI (aikau) mai nuhin mai magana.
Kun ga RAWANI kalma ce mai nuhin zawati ko kyalle na naɗawa ga kai, to amma idan muka walwale kalmar sai mu gane ma’ana da manufa. Kenan RAWANI al’adar hausawa ce, kuma ta ɗauko tushenta ne tun daga RA.

- Sakamako na huɗu, shi ne gadon sarautar mata ga hausawa. Tabbat, ikon Sarauniya SABA, Sarauniya DAURA, Sarauniya TAHAWWA, Sarauniya MANGOU, ba tatsinniya ba ce, gaskiya ne, kuma dukansu sun ɗauko tushensu ne daga RA.

- Sakamako na biyar shi ne jikokin waɗanda suka gina waɗannan daulolin na ƙasar Misira, waɗanda ake kira pyramide, na nan cikin Najeriya da Nijar.

- Sakamako na shidda, shi ne jikokin Nubiyawan farko, na nan cikin Najeriya da Nijar.

- Sakamako na bakwai shi ne yawancin sunayen ƙabiloli, hausa ce. Misali: SUMERIEN, AGADIEN, KANANEEN, ARAMEEN, MANDING, BAMBARA, KOTO KOLLI… ds.

- Yawancin sunayen ƙasashe, hausa ce. Misali: BABYLONIE, EGYPTE, HABASHA, SOMALIE, YEMEN, INDE …ds.

- Sakamako na takwas, shi ne ƙaryatar da tarihin hausa na banza bakwai da hausa bakwai.

- Sakamako na tara, shi ne ƙaryatar da ƙazafi da jahilci da ‘yan ƙar da ƙamzon kurege ke yi, cewa hausawa larabawa ne, ko kuma yawancin kalmomin hausa larabci ne.

Abin da ya kamata a gane shi ne, kafin Annabi Mohammadu (S.L.A.S) ya zo duniyar nan, har ya bayyana, akwai hausawa; kuma a san da sani cewa Annabi Mohammadu (S.L.A.S), annabi ne na ƙarshe sananne, kuma dalilin shi ne, harshe da addinin larabawa suka yaɗu, a lokacin nan tuni hausawa sun ƙaura.

Yaɗuwar addinin musulmunci, ko kuma jihadi da aka yi nan a ƙasashemmu na hausa, tsakanin junammu ne, baƙaƙe ; kuma yawancin mayaƙan ba su jin larabci, balle a ce an ci mu da yaƙi, kuma an bida mu da harshen larabci.

Akwai abu guda wanda lalle mun yi imani da shi, shi ne aro, ko kuma fanfaɗe da ke akwai tsakanin harshe da harshe, idan sun haɗu wuri guda.

To a faɗa muna inda hausawa suka zamna tare da larabawa a nan Afirka, har harsunansu suka shiga juna, inda hausa ta gaɓɓato, ko kuma ta zaɓɓato kalmomin larabci?

Haba jama’a, kar mu zama ‘yan amshin shata, ko kuma kwando abin zuba shara. Mu hankalta, mu nazarta, mu ƙwanƙwanta, mu maida niyya ga bincike domin fitar da takaici da jahilci, domin cin gaban kammu da kammu.

Da wannan gargadi muke dasa aya ga wannan babi, sai kuma mu gyara zama, mu karkaɗe kunnuwammu, domin sauraren babi na biyu, wanda ke ba mu bayani kan rubutun hausa, inda nan ma, za ku ji hikimar kakannimmu.
II./.RUBUTU
2.1. ALAMAR RUBUTUN FARKO
2.1.1/. RUBUTU SUMER

Rubutun farko a duniyar nan sananne, an same shi a cikin wata ƙasa wadda a ke kira MESOPOTAMIE, musamman ma a SUMMER.
(projection)

MESOPOTAMIE, kalmar Girkawa ce mai ma’ana MESOS (tsakkiya) POTAMOS (ruwa), wanda muke kira tsibiri da harshen hausa; tsibiri ko kalma ce wadda ta fito daga cibi RA; cibi RA na nufin wuri inda rana ta fara bayyana a cikin duniyar nan.

SUMMER ko, fassarar kalma ce mai faɗin daga inda masu rubutun suka fito. Sumer ko kalmar hausa ce mai nuhin bisa.

Ga wani dan misali, domin ku gane al’amarin:

- DU ga wannan kalmar an yi hoton tudu;
- SAG ga wannan an yi hoton kai tsaye;
- DU ga wannan an yi hoton tafiya ko gudu;
- KUR ga wannan an yi hoton duwatsu;
- TUM an ce ɗauka;
- DUDU an ce ƙafa, dudduge;
- GUB an ce tashi tsaye, ko kuma sa ;
- KI. an ce kibbiya ko kuma kihi.

Dukan waɗannan kalmomin, ba su da ma’ana ga larabci ko ga yahudanci, ko kuma ga duk harshen da kuke so, in ba harshen hausa ba; ku tuna da abin da muka shaida muku ɗazu. Don dai ku gane, kuma ku yarda, za mu shiga cikin ma’anar wannan kalmomin. Sai mu koma ga ma’ana ta sama.
2.1.2./. RUBUTU MAI LUNGU KO CUNEIFORME

Shi dai wannan rubutun ana kiran shi da sunan «écriture cunéiforme» ; wannan kalmar ta CUNEIFORME ta fito ne daga CUENUS mais nufin lungu, FORME (kama) ; a taƙaice dai wannan kalmar na nufin rubutu mai lunguna ko kuma mai kama da ƙusa ;

Ga dai alamar rubutun:
(projection)

Abin tambaya a nan shi ne: wace ƙabila ce ta ƙirƙiro wannan rubutun?

Masu ilimin bincike, sun faɗi cewa, wannan hikimar SEMITES ce, wato Yahudawa da Larabawa da saurensu, tunda su ne aka tarda a wurin. Amma inda abin yake da ɗarmun kai, shi ne yanda su magadan rubutun, ba su anfani da shi ta fuskar ƙere-ƙere ko sutura ko gini ko lamba ko shaidu…ds, har su bada gudummuwa ga ƙwanƙwancewa da fassarar rubutun .

Wannan lamarin ya ɗaure ma yawancin masu ilimin harshe kai, ko kuma masu nazari. Wannan hanyar da suka ɗauka, ba ta dace ba , shi ya sa waɗansu masu hankali, kamar Jean BOTTERO, sun yi watsi da lamarin, inda suka ce ya kamata a maida bincike bisa ga wasu ƙabilu inda waɗannan kalmomin za su samu ma’ana cikakka. Wannan daidaituwar, za ta bunƙasa, kuma za ta ƙarfafa wannan ilimin da ake kira archeologie, wato (ilimin kufai).

A fuskar rubutun, gogayen aikin sune :

Ø SIR WILLIAM FLINDERS PETRIE (1905);
Ø A.H.GARDINER, (1915);
Ø ALBRIGHT, (1948);
Ø CLAUDE SCHAEFFER; (1929)…ds.

A nan, sakamako ya rinjaya ne ga yanda mutanen ke anfani da laka ta fuskar rubutu, ko kayan aiki ko na ƙawa da saurensu. Waɗannan abubuwan namu ne, tunda har kwanan gobe, za mu yi anfani da su. Akwai wasu abubuwa waɗanda aka binciko a nan ƙasashemmu na Afirka masu kama da hakanan. Idan ko haka gaskiya ne, to biri ya yi kama da mutum.

A cikin wani littafi mai suna « tsakanin adali da rubutu , shekara ta 1994» da malam JACK GOODIE ya gabatar, mun samu wurin da aka ba mu bayani kan wannan rubutun, cewa ya ƙumshi babbaƙu talatin da biyu (32). Su dai waɗannan babbaƙun ana rubuta su ne daga hauni zuwa dama, kuma sun fito ne daga cikin na Kanana ainahi tun ƙarni goma sha hudu kahin aihuwar annabi ISA (T.A.T.A.).

Shi kuma wannan rubutun ya aifar da na PHENICIENS, mai babbaƙu ishirin da biyu (22) ; su kuma Yahudawa da Girkawa, sun ramta daga gare su wajen ƙarni goma sha ukku.

2.1.3./. RUBUTU HIEROGLYPHE

Idan kuma mun komo ga wannan rubutun HIEROGLYPHE, wato HIERO (sacre: tsarkakke) GLYPHE (écriture: rubutu), sai mu gane da cewa duk waɗannan kalmomin, na harshen Girkawa ne, ke nan rubutu ya rinjaye su; Idan ko haka gaskiya ne, abun tambaya a nan shi ne: shin wai su masu yin wannan rubutu, farfaru ne ko baƙaƙe? Ƙaƙa suke kiran rubutun? Ba a yin la’akari da wannan damuwar, sai dai a cilasta muna da ƙarya.

Ba za mu yarda ba, kuma da iznin Allah za mu ci gaba da bincike don ci-gaban kammu da kammu.
2.2./. ALAMAR BABBAƘUN DUNIYA

Alamar babbaƙun duniya ta kasu gida biyu : akwai na farar fata, kuma akwai na baƙar fata.

2.2.1./. BABBAƘUN FARAR FATA

2.2.1.1./. EGYPTE

A. I. Y. Y. W. W. B. H. P. F. M. M. N. R. H. H. H. H. S. S. CH. K. K.F. G. T. TJ. D. DJ.

(projection)
2.2.1.2./.COPHTE

A. V. G. D. E. S. Z. I. TH. I. K. L. M. N. X. O. P. R. S. T. E. F. CH. PF. O. SC. F. CH. H. G. SC. D.

(Projection)

2.2.1.3./. GREC

Babbaƙun grec sun kasu gida ishirin da huɗu (24); ga yanda suke:
A .V.G. D. E. Z. I.TH. I. K. L. M. N. X. O. P. R. S. T. Y. PH. CH. PS. O.

Idan muka lura, a cikin babbaƙun, babu waɗansu, kamar su B. C. F. G. H. J. Q. U. W.Y.

(projection)

A game da ainahin waɗannan babbaƙun, ra’ayi ya kasu gida biyu:

Ø Waɗansu kamar GELB sun ce an ƙirƙiro su a Grece wajen 750 kahin aifuwar Annabi ISA;
Ø Waɗansu ko sun ce Samidawan yamma ne suka ƙirƙiro su wajen 700 kahin aifuwar Annabi ISA.

A game da babbaƙun, abin da Girkawa suka yi, shi ne ƙara hikima ga wasulla daidai da harshensu.

Idan muka dawo kan babbaƙun, za mu gane da cewa, Girkawa da Samidawa sun yi abun ga da hausawa ke cewa “hankaka maida ƙwan wani naka”. Waɗansu masu hankali, kamar su COLDSTREAM 1977, HAVELOCK 1973, GOODY da WATT 1963, sun ce wannan zance bai dace ba; Inda rubutu ya fito ainahi, shi ne ASIE MINEURE. Sun ƙara da cewa babbaƙu da tsari da kamar babbaƙu, aikin mutane ne masu magana da harshen KANANA, harshen Samidawa.

Kash! Ga zance ya bi hanya to amma sai ya ratse, tunda cikin sarakunan gobirawa sanannu, akwai na farin mai suna KANANA, Gobirawa ko baƙaƙe ne. Idan ko haka gaskiya ne, Kananawa ba Samidawa ba ne, ba Larabawa ba ne, ba Yahudawa ba ne, ba Geze ba ne, ba ma Kiyaya ba ne , manoma ne, kuma suna cikin zuri’ar jikokin Annabi Nuhu (T. A..A.S.T.G.).

2.2.1.4./. LATINA
A. B. G. D. E. V. Z. K. L. M. N. O. R. T.
(projection)

2.2.1.5./. YAHUDAWA

Babbaƙun Yahudawa talatin da ɗaya ne; ga dai kamanninsu:

A. B. V. G. D. H. W. Z. H. T. Y. K. KH. K. L. M. M. N. N. S. A’. P. F. F. TS. TS. K. F. SH. S. T.
(projection)
2.2.1.6./. LARABAWA
A. B. T. TS. DJ. H. KH. D. Z. R. Z. S. SH. S. DH. T. Z. A’. GH. F. Q. K. L. M. N. H. W. Y.
(projection)

2.2.1.7./. ETHIOPIE

H. I. H. M. S. R. S. S. Q. B. T. TCH. H. N. GN. A. K. H. W. A. Z. S. Y. D. J. G. T. TCH. P. S. S. F. P.
(projection)

2.2.1.8./.LYBIQUE
B. G. D. W. Z. Z. Z. T. I. K. L. M. N. S. S. F. C. Q. R. S. T. T.
(projection)

2.2.1.9./. TIFINAGH

B. CH. D. D. F. G. DJ. H. I. J. K. O. KH. L. M . N. W. R. S. T. T. Z.
B. G. D. H. W. Z. H. T. Y. K. L. M. N. S. G. S. Q. R. S. T. F. G. Z. D. D. Z. H.
° = a; é; e; i
(projection)


Abin da ya kamata a lura da shi a nan, shi ne yanda babbaƙun suke:
Ø zube barkatai;
Ø ba tsari;
Ø ba ma’ana;
Ø ba a san ba wanda ya ƙirƙiro su;
Ø waɗansu sun fi waɗansu yawa ;
Ø babu cikakkun wasullai ;
Ø babu ayoyi
Ø babu langayen wasullai ;…ds.

Ko wannan al’amarin ne ya sa, watakila, ake kiran rubutun zamani da sunan « écriture conventionnelle : rubutu na yarjejeniya » ?

2.2.2./. MA’ANAR BABBAƘUN A JIMILCE

ALEPH na nufin “sa” da harshen semitique, wannan baƙi babu shi ga harshen Girkawa, amma sun ɗauke shi kamar «a» ;

BET: na nufin “gida” ko “tanti”, kuma ma’anar shi “b”;

GAML: na nufin “raƙumi”, ko kuma “tozon raƙumi” g;

DELT: na nufin “ƙofa” d;

HE: babu ma’ana h;

WAU : na nufin “kusa” ko kuma “ijiyar sau”; babu shi da harshen Girkawa:

ZAI : na nufin “icce mai bada olive”;

HET: na nufin « katanga » ko «shimge» ;

TET : babu ma’ana ;

YOD : na nufin « hannu » ;

KAF: na nufin « tahin hannu » ;

LAMD: babu ma’ana;

MEM: na nufin “ruwa”;

NUN : na nuhin “kihi”;

AIN: na nufin “ijiya”;

PE : na nufin “baki”;

SADE :na nufin “ɗan fatsa” ko “lauje” ko kuma “hanci”;

QOF: babu ma’ana;

RES: na nufin “kai”;

SIN : na nufin “haƙori”;

TAU : na nufin “shaida” ko kuma “lamba”.

Idan aka jimilta waɗannan babbaƙun, sai mu ce su ishirin da ɗaya ne (21); waɗansu na da ma’ana, kuma waɗansu ba su da ma’ana;

Abin da muka gane a nan , shi ne: harsuna ukku ke anfani da waɗannan babbaƙun: akwai yahudanci, akwai larabci, akwai misiranci. Misiranci ko ba harshen semites ba ne, kamar yanda ake kirari cewa babbaƙu ko kuma alphabet aikin Samidawa ne. Abun tambaya a nan shi ne, yaya ake ƙera abun da ba ya da suna, ba ya da ma’ana?

A nan ma, ya isa mu gane da cewa, alphabet dai, ba aikin Samidawa ne ba, kuma ba aikin Turawa ne ba; idan haka gaskiya ne, to ina ya kamata mu maida bincike da nazari kan asalin rubutu, ko kuma asalin alphabet ?

Tunda su dai Shinuwa (mutanen Sin) da Indiya (mutanen Hindu) ba su da alphabet, ai sai mu nuho Afirka, baƙar fata, mu gani ko!

To haka ɗin ba ta faru ba; ke nan dai, sun sani, don wannan ne, ta wani fanni, ake gallaza muna, ake sa muna yunwa da ƙishirwa, da yaƙi da sauransu, don kar mu ci gaba! Abun tambaya a nan shi ne : shin wai wannan rubutun da su Turawa da Larabawa da sauransu ke tamaƙa da kuri da shi, daga ina ya fito ? To a nan ne babbar hikimar wannan sakamakon bincikemmu da nazari kan rubutun hausa da za mu ba ku zuwa gaba idan Allah Sarkin sarauta ya yarda.

Kafin ranar za mu ba ku ɗan bayani kaɗan ga ma’ana da fassara kan babbaƙun latina ko na larabci, kamar dai yanda Turawa masu bincike da nazari kan lamarin suka faɗi ; Ga wani ɗan misali wanda LOUIS-JEAN CALVET, Farfesa na ilimin al’umma da harshe na Jami’ar SORBONE ya bada a cikin littafinsa mai suna « HISTOIRE DE L’ECRITURE : Tarihin Rubutu», FEVRIER 1997:

Idan muka gane da cewa baƙi ya fito daga hoton abubuwa, to a nan ma, waɗansu babbaƙun, ba su da tushe; yaya aka yi haka? Zancen ga ko akwai gaskiya dai? Idan muka ɗauki ɗan misali kaɗan kan babbaƙun (aleph da delt), sai mu ce akwai duhu cikin lamarin;

Kowa ya san Larabawa da Yahudawa ba makiyayan shanu ne ba; ba su da shanu duk duk duk; To daga ina ne “sa” ya fito har yake nufin “a”?

To amma inda wannan lamari zai fi dacewa, da inda zai fi ma’ana sai ga HAUSAWA (masu hawan shanu); wanda ko ba ya da sa, ba shi hawan sa, balle ya yi zancen sa! Ke nan wannan baƙi, cewa da A, tushen alphabet, magana ce a dunƙule, mai nufin masu shanu mafarin alphabet, biri ko ya yi kama da mutun; za ku samu ƙarin haske zuwa gaba, bayan exposition (nuni) da iznin Allah !

Baƙi na biyu wanda muka ɗauka don misali, shi ne DELT; shi dai wannan baƙin an ɗauke shi kamar ƙofa mai lungu ukku. Abun tambaya a nan shi ne: wane irin gida ne mai wannan ƙofar, wanda ya dace da tabi’o’in makiyaya, masu gidan fata? Wannan ma’ana dai ba ta dace ba, kuma haka dai ake yi domin a ɓatar da mu, a ƙara tura mu cikin daji.

Kun ji kuma kun gani, yanda ake horon mu da cewa rubutu, aikin makiyaya ne, musanman Larabawa da Yahudawa. Akwai gaskiya ko ? Amsa na gare ku matasa.

Abin da muka amince ma, shi ne yanda babbaƙu ke fitowa daga hoto; amma fassara da ma’ana da tushen babbaƙu na latina da na larabawa da yahudawa, ba mu amince ba, kuma za mu yi yaƙi matuƙa kan lamarin har gaskiya ta tabbata da iznin Allah !

Ga dai wani ɗan misali tamkar shirme wanda shi wannan baturen, Farfesa CALVET, ya rubuta kan ainahin baƙi.

(projection)

Na ɗaya, ya ɗauki hoton rana, wanda ake kira da sunan “soleil” da harshen faransanci, “solej” da wani harshe.

Na biyu, ya ɗauki hoton rana, wanda ake kira “ra” da harshen mutanen Misira, wanda ya kira copte, “soleil” da harshen faransanci. Sai ya ce waɗannan misalan biyu, ba su da dangantaka, kuma ba su kama da juna ta fuskar ainahin baƙi.

Wacce ce hujjarsa, tunda ya ce wannan kalmar ta mutanen Misira ce, ai akwai su can dauri, ya tambaye su mana, ya ji ma’ana ko kuma fassarar “ra”, in dai har binciken gaskiya ne yake yi, ai zai gane kurensa, domin ƙarin haske kan lamarin, to hakanan ɗin ba ta faru ba, don son rai, don son suna da girman kai.

Akwai dangantaka ƙwarai tsakanin misalan biyu, kuma suna kama da juna ta fuskar ainahin baƙin. Idan ba ku manta ba, ai “ra” rana ce ko, kuma mun gani yanda wannan kalmar ta “ra” ta ba mu kalmomi, da sunaye da karin magana a cikin harshen hausa; Kuma harshen hausa kaɗai ya kai hakanan, wanda duk ya yi gardama ya jarraba ya gani.

2.2.3./. BABBAƘUN BAƘAR FATA

A game da rubutun duniya, Turawa sun ce, kowace ƙabila ta gwada hikimarta kan lamarin ; To amma shi baƙin mutum, iliminsa bai ba shi wannan fusa’ar ba ; Wannan ƙazafi ya damu wasu Afirkawa, inda suka ƙirƙiro rubutu iri-iri, kamar haka:

(projection).

2.2.3.1/. WOLOF

A. C. M. K. B. MB. J. NJ. S. W. L. G. NG. N. D. ND. X. H. Y. T. R. N. F. N. R.

2.2.3.2./. MASABA

P. T. C. K. B. D. J. G. F. S. NZ. M. N. NY. N. Y. W. H. L. R.

2.2.3.3./. MANENKA

H. P. R. DY. TY. D. R. S. GB. F. K. L. M. NY. N. H. W. Y.

Abun takaici a nan , shi ne duk da kishin da waɗannan Afirkawa suka yi, rubutun nasu bai samu martaba ba kuma bai samu karɓuwa ba ga ma’ikontammu da mutane.

A game da ainahin babbaƙu da ma’anarsu, mun gano da cewa zama dai bai same mu ba, don haka muke cewa a sake bincike.
III./. A SAKE BINCIKE KAN RUBUTUN AINAHI
3.1./.AINAHI KO TUSHEN RUBUTUN HAUSA

Shi dai wannan rubutun, mun same shi ne ga wani bawan Allah, a jahar MARADI, ƙaramar hukumar Dakoro, jamhuriyar Nijar.

Wannan bawan Allah, bahaushe ne, bagobiri; Sunansa DOGUWA MAI WASA (Allah ya jiƙan shi. Amin). Manomi ne, kuma mahalbi ne. Ya gadi wannan rubutun ga kakansa, shi kuma ya hori jikansa mai suna ADARE SALIHU. Shi kuma Adare Salihu ƙane ne gare ni.
3..2./. ANFANINSA

Ana anfani da wannan rubutun ta fuskar bambanta magungunan gargajiya.

3..3./. ALAMAR RUBUTUN HAUSA

Babu shakka hausawa na da rubutu, wanda ke ƙumshe da ma’ana, da hikima, da ƙayatarwa.
Ga alamar rubutun:
(Projection)

Rubutun hausa na ƙumshe da abubuwa guda biyar masu ɗimbin ma’ana:
3.4./. YANAYIN FURUCIN HAUSA

Kafin mu ba ku bayani dalla dalla, muna son mu fara da yanayin furuci na harshen hausa.
Harshen hausa na da yanayin furuci guda goma sha ɗaya (11):
- Akwai zuzau
- Akwai tunkuɗau
- Akwai ragaɗe
- Akwai ragare
- Akwai tsayau
- ds…
3.5./. BABBAƘUN HAUSA

Idan ana son a jimilta babbaƙun hausa, sai mu ce su arba’in da ɗaya ne (41). Yaya ne su babbaƙun ke gudanar da rayuwarsu ? Sai ku saurare mu da kyau.

Babbaƙun hausa sun kasu gida biyu :
- Akwai maza ;
- Akwai mata ;
- Akwai manya ;
- Akwai ƙanana.

Idan kuma muna son mu kwatamta babbaƙun hausa, sai mu ce al’amuransu ɗaya suke da duk halittar Allah. Tunda mun shaida muku da cewa a cikin babbaƙun hausa akwai maza kuma akwai mata, to ku san da sani aure zai wanzuwa tsakaninsu, inda a cikin arba’in da ɗaya, takwas aifaffi ne. Wannan lamarin na babbaƙun hausa, zai ba mu damar ganewa da wannan hikimar ta bambanta namijin kalma da tamatan kalma (wanda ake kira a turanci genre), tunda kalmomin da babbaƙu aka yi su; Wannan wani abun ƙayatarwa ne ga masu ilimin harshe, inda har yanzu ba su hango ba da cewa a cikin babbaƙu, akwai maza kuma akwai mata. Dukansu babbaƙun, kowanne da sunansa, kuma da ma’anarsa.

3.5.1./. WASULLAN HAUSA

Bayan babbaƙun hausa, akwai wasulla. Dukan tursassan wasullan hausa su bakwai ne (7); Kowane wasali da sunansa kuma da ma’anarsa.

3.5.2./. LANGAYEN WASULLAI

Alamar rubutun hausa ta ukku, ita ce langayen wasullai. Su ma sun kasu gida bakwai; a cikinsu akwai masu tafiya da manyan babbaƙu, kuma akwai masu tafiya da ƙananan babbaƙu. A nan ma, kowane langayen wasali da sunansa da ma’anarsa, kuma da aikin da yake yi bisa ga kowane baƙi.

3.5.3../. GOYON WASULLAI

Akwai goyon wasullai, su ma su tara ne (9). Akwai ‘yan biyu, akwai ‘yan ukku, akwai ‘yan huɗu.

3.5.4./.AYOYI

Alama ta huɗu ita ce ayoyin hausa. Ayoyin rubutun hausa sun kasu gida goma (10), kuma kowace aya na da sunanta da ma’anarta, da aikin da take yi a kan kowace sheɗara ko jumla.

3.5.5./. ‘YAN LISSAFI

Alama ta ƙarshe ita ce ta ‘yan lissafi, su kuma sun daidata kan gida tara (9). Kowane ɗan lissafi na da sunansa da ma’anarsa.

3.5.6./. WAKILLAN ‘YAN LISSAFI

Wakillan ‘yan lissafin Hausa kala biyar ne (5): akwai ‘yan ragau, akwai ‘yan ƙarau, akwai ‘yan ruɓanyau, akwai ‘yan raɓau, akwai ‘yan daidaitau.

TAƘAITAWA
Ga wata tambaya, jama’a: shin wanda bai san ba daga inda ya fito, ƙaƙa za ya sanin kansa, har ya san manufa, har ya yi zancen wani? Saboda haka, dangi ‘yan uwa, muna kira gare ku: mu farka, mu tashi tsaye, mu so junammu, mu rungumi junammu, mu haɗa kanummu, mu yaƙi jahilci da talauci da sauransu, domin ci-gabammu da kammu, domin rayuwarmu da kammu, domin tsirar kammu da kammu.

A nan za mu dasa aya kan rubutun hausa, sauran bayani sai ranar bikin nuna ma duniya rubutun (exposition).





































BIBLIOGRAPHIE

1/.LA BIBLE

2/. BOUBOU HAMA, «Histoire du Gobir et de Sokoto», Présence Africaine, 1967

3/. C HARLES HOUGOUGNET «L’écriture», édition PUF

4/. CLAIRE LALOUETTE, «Au royaume d’égypte, le temps des rois-dieux», éd. Fayard 1991.

5/. CHAICK ANTA DIOP, «nations nègres et cultures», Présence Africaine, 1979

6/. CHAICK ANTA DIOP, « L’unité culturelle de l’Afrique noire », Presence Africaine, 1982

7/. CHAICK ANTA DIOP, «Parenté génétique de l’égyptien pharaonique et des langues négro africaines», NEA, 1977

8/. DOMINIQUE SOURDEL, «Histoire des arabes», Que-Sais-Je, PUF, 1985

9/. GEORGES ROUX «La mésopotamie», Seuil, 1995

10/. GERARD NAHON, «Les Hebreux», édition seuil

11/. JACK GOODY «Entre l’oralité et l’écriture», PUF, Juin 1994

12/. JEAN BOTTERO et MARIE JOSEPH STEVE «Il était une fois la mésopotamie», édition découvertes Gallimard, 1993.

13/. JEAN DORESSE, «L’empire du Pretre Jean, l’éthiopie antique», édition plon, 1957

14/. LOUIS JEAN- CALVET «L’histoire de l’écriture»,Plon, 1996.

15/. FRANCIS AUFRAY, «Les anciens éthiopiens», édition Armand Colin, Paris 1990

16/. LE SAINT CORAN

17/. HIRA DA :

KORAU ANGO;
DOGUWA MAI WASSA;
ADARE SALIHU.

Saturday, January 17, 2009

Wakar Haduwar so ko Takaici.


HADUWAR SO KO TAKAICI ?

1. Bismillah Allah rahimi
Sarkin da yai ]ari har ]umi
Kuma yai kyawu da tsarin hurrumi
Irin su Halima mai kyawun tsegumi


2. Allah Salatinka marar adadin fa]a
Gareshi Kykkyawan da Yazzarce fa]a
[an Amina mai kyawun da kowa kan fa]a
Kyawunsa ba ya shi kuje ku yi tsegumi



3. Gabana yakan fa]i da na tuna
Juma’a ta disamba da mintuna
Sha takwas bisa hu]]u nakan tuna
Gamona gareki mai kyawun tsegumi


4. Da a kwai hurul’aini a duniya
Da nai rantsuwar ganin shugabarsu da ijjiya
A tashar magamar nan ta Jibbiya
Mai gashin da yaffi na Hindu kuje kui tsegumi


5. Muryarta za}inta ya zarce nazzuma
Balle idanun nan nata na hikkima
Masu farin da yazzarce na gwal ba gardama
Kyawun Halima yazarta fagen yin tsegumi


6. Iska da yagganta yaja tunga yattsaya
Domin }urarsa tana shakkar kyakkyawa yattsaya
Yana kallon kansa cikinta gilashin duniya
Ya ga tauraruwar mata mai kyawun tsegumi


7. Fatar Halima tafi Madubi dan ku ji
Kyawun idanta ya zarta na gwal kowama ya ji
Babu ‘yar da ta kaita }ira wannan ma kuji
Balle kykkyawan bakinta da yassha tegumi


8. A tsaye na isheta tana juro
Mota ta kattsina gurin juro
Ta haska mutan gun sun turo
Idaunsu a kanta suna yin tsegumi

9. Mota ta ishemu nan tattsaya
Muka shisshiga kowa ban tsaya
A kussa da ni nan tattsaya
Wannan ce Halimar da kowa ke mata tsegumi


10. Kyawun Halima babu na Algusu
Ta zarta duk wata ‘ya bana musu
Ina kyawawa duk kubar musu
Shugabarku Halima kuje ku yi tsegumi


11. {wakwalwata nan tammace
Zuciyata ta yi zubar ice
Kunnnuwana sun kakkarkace
Da jin muryarta ina maku tsegumi


12. Ka basu ku]inka ta zan fa]a
Na mota zasu su har ha]a
Ni bani da canji zan fa]a
Sai na canza nai maka tsegumi


13. Da nawa da nata nazan biya
Kyakkyawa tayyi ta godiya
Hada sambarka duk ta iya
Shugabar kyawawa in yi maku tsegumi

14. Mota ta ajemu cikin alfahari
Ta kalleni kallon fahari
Na yarda da kai ]a mai fahari
Halima taffada kuje kuyi tsegumi

15. Sunana Halima ta zan fa]a
Naka sunan zan so kaffa]a
Harda lambata zan harha]a
Maka nasan kaso tsegumi

16. Rabe Kai ]ane mai kwarjini
Zuciyata ta yi nitson gani
Ta soka irin so naggani
Na’auwa sonka na yi mani tsegumi

17. A nan bankwana ta yi mani
Da salama har ta raka mani
Muna ta nisha]i ba hani
Da kykkyawa mai kyan tsegumi

18. Mai }irar da babu kama tata
Kaf duniya ba mai tsari nata
Balle kunya ta kyan hali nata
Kaga mai ilmin da yazzarce tegumi

19. Shugabar kyawawan duniya
Masu ajin tin}ahon duniya
Kin fisu ajin duk duniya
Gaba]ayansu suna yin tsegumi


20. Du kwakwazon da ake kan [awisu
Na kyau da zubinasa ]awisu
A farcenta ya san kyawu nasa ]awisu
Har yake tin}aho in maku tsegumi


21. Na yi kuka har nayi jan ido
Don takaici har bana ado
Zuciyata ta yi rashin bi]o
Lamba tata jigon tsegumi


22. Babu Jawwal domin na rasa
Jigon ha]uwarmu yau na rasa
Hanyar ganintamma na rasa
Yau ba Halima balle in tsegumi


23. Kaga wadda jininmu ya zam ]aya
Tsoka ta jiki har jijiya
Na rantse Gaba]aya kujjiya
Don ni aka yita mai kyawun tsegumi


24. Babu ni yau in har ba ita
Ruhina ya tsere don ita
Ya barni duk domin ita
Ita ce rayina ku je ku yi tsegumi


25. Jama’a kuyo mani agaji
Ku tallafi rayina domin agaji
Halima ce Burina don kuji
In na ganta na warke sai yin tsegumi


26. Halima in babu ke kinsan babu ni
Tafiya ma kin san banda ni
{unci da kuka su suka tada ni
A kanki yau nazan ban tsegumi


27. Inama burina zai cika
Ki dawo gareni Lallai zan cika
Da farin ciki murna ta cika
In yi tsalle har ma in tsegumi


28. Allah kasa in ganta ni
Koda a Mafarki ba Hani
Halima Dan Allah dawo kin sani
So da }aunarki su naka Tsegumi


29. Tammat jama’a nan zan tsaya
Don kyaleku fa yassa zan tsaya
Ga Halima kam babu batun tsaya
Yanzu na fara sonta kuje ku yi tsegumi


30. Bissalam da salama ‘yan uwa
Ku tayani du’ai kan ‘yar uwa
In ganta ta zamto min uwa
Ga ‘ya’yayena ba yin tsegumi


31. Godiya Ga Jalla abin yabo
Da ya bani ikon yin yabo
Ga Halima kyakkyawa sha yabo
Halima kam kowa na mata tsegumi

32. Ga mai son sanina yau ya san
Rabi’u Sunana Ban nusan
Kano nake biget ko kasan
Taimakona kanta mai kyan tsegumi

Wakar Mayaumasoyiya Wakar da na rubuta a Birnin Ouagadougou Burkina Faso

Daga
Comrade Rabi’u Na’auwa
Daga Birnin Ouagadougou Burkina Faso

Bissalam salama a gareki masoyiya a yau zan barki

1. Ya Allahu ya ahadu samadu
Lam ya ld walam yu ladu wahidu
Sarkin nan guda wanda yayo du
Duniya Rahimu ya kageni

2.Allahumma salli wala adadu
Wanda ba ya shi kuma har abadu
Bashi yaudara shi Muhammadu
Kinga yau mayau ni kin barni

3. Nai salati gun baban zahra
Jarumi maki gunta yaudara
Yayi tur da hali na yaudara
Amma kinka aikota gareni

4.Na iso cikin gaggawar
Domin ganinta nake sha’awar
Yan uwa kuyi mani ta’aziyar
Domin masoyiya ta barni

5.Mayaumasoyiya ta barni
gashi sonta ya kamani
Rashin sani ya kwareni
Da na barta tun tuni babu sani

Ki tuna fa ni ne mai sonki
Mai zurfafawa kan sonki
Mai yin bajintar kaunarki
Kin manta wannan kin barni

Ki tuna batun alkawarinmu
Na ranar nishadinnan tamu
Juma’a ta zamto ranarmu
A gidanku amma kika barni

Ashirin da huddu fa su na tuna
Ga augusta na san zaki tuna
Kika dauki alkawari ki tuna
Amma kinka karya kika barni

Ki tuno kalaman nan naki
Baki yaudara a kalamanki
Baki cin amanar kaunarki
Gashi kinci tawan kin barni


To gashi yau kinci amana
Ki tuno da sonmu fa na amana
Alkawar fa kaya ne ki tuna
Kin karya shi yau kin barni

Ki tunafa ni ne nassoki
Naki tanka kowa dominki
Na bayar da kaina a gareki
Hally a yau kin barni

Ki tuno da ranar soyayya
Wadda munka yita a can baya
Ki tuno nishadinmu na baya
Kin zubda shi yau kin barni

Kin butulci fannin soyayya
Kin karya darajar soyayya
Kin yaudara bisa soyayya
Tinda gashi kin yita gareni

Ki tuno nasiharki garemu
Dadi ko wuya mu rike kanmu
Mu rike amanar junanmu
Har mu cimma buri babu hani

Gashi dukka kin ture wannan
Babu kuskure daga ni dinnan
Ke kinka furta kalaman nan
Ofishinku ban manta ki sani

Zai kyau ki san son alkawari
Bashi saiduwa don dinari
Masoya kuzan cika alkawari
Ku rikeshi ba ji babu gani

Gashi na rikeshi daram ku sani
Mayaumasoyiya ce ta gujeni
Ta kareshi kal domin ku sani
Babu so a yau ta barni

Sai mu daina koyi da irinsu
Kunga duniya ta rudesu
Mu mu bita sannu fa ya nasu
Na garinmu balle yan birni

Zai kyau gaba daya muyi nazari
A duniya mu yi Alkairi
Don lahira muga alkairi
Kin manta wannan kin barni

Yanzu dai nasiha zan yi maki
Ki rike mijinnan naki
Domin ki san Aljannarki
Na gareshi ban son yai yi hani

Zaifi kyau ki san soyayya
Bata bin tunanin dukiya
Lallai mubar son zuciya
Dube misali kin gujeni

Arrahimu nai yi kira Jalla
Ka haneni yaudara duk wahala
Ka tsaremu fadawa wahala
Don Hally yau ta barni

Gani yau a Burkina ba wahala
Wagaduggu naccika su jumla
Baitocinga sun ka zamo jumla
Ashirin da huddu ku zamfa sani

Alhamdu Jalla gwani nawa
Da ka bani ikonjurewa
Na yi baituka ga mayau tawa
Da ta yaudareni ta cuceni.