Saturday, January 17, 2009

Wakar Haduwar so ko Takaici.


HADUWAR SO KO TAKAICI ?

1. Bismillah Allah rahimi
Sarkin da yai ]ari har ]umi
Kuma yai kyawu da tsarin hurrumi
Irin su Halima mai kyawun tsegumi


2. Allah Salatinka marar adadin fa]a
Gareshi Kykkyawan da Yazzarce fa]a
[an Amina mai kyawun da kowa kan fa]a
Kyawunsa ba ya shi kuje ku yi tsegumi



3. Gabana yakan fa]i da na tuna
Juma’a ta disamba da mintuna
Sha takwas bisa hu]]u nakan tuna
Gamona gareki mai kyawun tsegumi


4. Da a kwai hurul’aini a duniya
Da nai rantsuwar ganin shugabarsu da ijjiya
A tashar magamar nan ta Jibbiya
Mai gashin da yaffi na Hindu kuje kui tsegumi


5. Muryarta za}inta ya zarce nazzuma
Balle idanun nan nata na hikkima
Masu farin da yazzarce na gwal ba gardama
Kyawun Halima yazarta fagen yin tsegumi


6. Iska da yagganta yaja tunga yattsaya
Domin }urarsa tana shakkar kyakkyawa yattsaya
Yana kallon kansa cikinta gilashin duniya
Ya ga tauraruwar mata mai kyawun tsegumi


7. Fatar Halima tafi Madubi dan ku ji
Kyawun idanta ya zarta na gwal kowama ya ji
Babu ‘yar da ta kaita }ira wannan ma kuji
Balle kykkyawan bakinta da yassha tegumi


8. A tsaye na isheta tana juro
Mota ta kattsina gurin juro
Ta haska mutan gun sun turo
Idaunsu a kanta suna yin tsegumi

9. Mota ta ishemu nan tattsaya
Muka shisshiga kowa ban tsaya
A kussa da ni nan tattsaya
Wannan ce Halimar da kowa ke mata tsegumi


10. Kyawun Halima babu na Algusu
Ta zarta duk wata ‘ya bana musu
Ina kyawawa duk kubar musu
Shugabarku Halima kuje ku yi tsegumi


11. {wakwalwata nan tammace
Zuciyata ta yi zubar ice
Kunnnuwana sun kakkarkace
Da jin muryarta ina maku tsegumi


12. Ka basu ku]inka ta zan fa]a
Na mota zasu su har ha]a
Ni bani da canji zan fa]a
Sai na canza nai maka tsegumi


13. Da nawa da nata nazan biya
Kyakkyawa tayyi ta godiya
Hada sambarka duk ta iya
Shugabar kyawawa in yi maku tsegumi

14. Mota ta ajemu cikin alfahari
Ta kalleni kallon fahari
Na yarda da kai ]a mai fahari
Halima taffada kuje kuyi tsegumi

15. Sunana Halima ta zan fa]a
Naka sunan zan so kaffa]a
Harda lambata zan harha]a
Maka nasan kaso tsegumi

16. Rabe Kai ]ane mai kwarjini
Zuciyata ta yi nitson gani
Ta soka irin so naggani
Na’auwa sonka na yi mani tsegumi

17. A nan bankwana ta yi mani
Da salama har ta raka mani
Muna ta nisha]i ba hani
Da kykkyawa mai kyan tsegumi

18. Mai }irar da babu kama tata
Kaf duniya ba mai tsari nata
Balle kunya ta kyan hali nata
Kaga mai ilmin da yazzarce tegumi

19. Shugabar kyawawan duniya
Masu ajin tin}ahon duniya
Kin fisu ajin duk duniya
Gaba]ayansu suna yin tsegumi


20. Du kwakwazon da ake kan [awisu
Na kyau da zubinasa ]awisu
A farcenta ya san kyawu nasa ]awisu
Har yake tin}aho in maku tsegumi


21. Na yi kuka har nayi jan ido
Don takaici har bana ado
Zuciyata ta yi rashin bi]o
Lamba tata jigon tsegumi


22. Babu Jawwal domin na rasa
Jigon ha]uwarmu yau na rasa
Hanyar ganintamma na rasa
Yau ba Halima balle in tsegumi


23. Kaga wadda jininmu ya zam ]aya
Tsoka ta jiki har jijiya
Na rantse Gaba]aya kujjiya
Don ni aka yita mai kyawun tsegumi


24. Babu ni yau in har ba ita
Ruhina ya tsere don ita
Ya barni duk domin ita
Ita ce rayina ku je ku yi tsegumi


25. Jama’a kuyo mani agaji
Ku tallafi rayina domin agaji
Halima ce Burina don kuji
In na ganta na warke sai yin tsegumi


26. Halima in babu ke kinsan babu ni
Tafiya ma kin san banda ni
{unci da kuka su suka tada ni
A kanki yau nazan ban tsegumi


27. Inama burina zai cika
Ki dawo gareni Lallai zan cika
Da farin ciki murna ta cika
In yi tsalle har ma in tsegumi


28. Allah kasa in ganta ni
Koda a Mafarki ba Hani
Halima Dan Allah dawo kin sani
So da }aunarki su naka Tsegumi


29. Tammat jama’a nan zan tsaya
Don kyaleku fa yassa zan tsaya
Ga Halima kam babu batun tsaya
Yanzu na fara sonta kuje ku yi tsegumi


30. Bissalam da salama ‘yan uwa
Ku tayani du’ai kan ‘yar uwa
In ganta ta zamto min uwa
Ga ‘ya’yayena ba yin tsegumi


31. Godiya Ga Jalla abin yabo
Da ya bani ikon yin yabo
Ga Halima kyakkyawa sha yabo
Halima kam kowa na mata tsegumi

32. Ga mai son sanina yau ya san
Rabi’u Sunana Ban nusan
Kano nake biget ko kasan
Taimakona kanta mai kyan tsegumi

No comments:

Post a Comment