Sunday, January 25, 2009

ASALIN HAUSAWA DA RUBUTUN HAUSA NA AINAHI


ASALIN HAUSAWA DA RUBUTUN HAUSA NA AINAHI
DAGA
DOKTA KORAO H. MAHAMADU











LAkCAR DA AKA GABATAR A ƘARƘASHIN
INUWAR KWAMITIN ƘASA (NAJERIYA)
KAN NAZARIN HARUFFAN HAUSA









WURI: BABBAN DAKIN TARO
JAMI’AR JAHAR KADUNA, KADUNA

RANA: LITINI, 24 GA YULI, 2006

LOKACI: 10:00 NA SAFE



ABIN DA KE CIKI

GABATARWA……………………………………………………………………………………… ………….2
I./. HaRshen hausa. 3
1.1./.Da kalmar RA. 4
1.2./. Da kalmar RE. 4
1.3./. SAKAMAKO.. 5
1.3.1./. SAKAMAKO KAN HARSHE. 5
1.3.2./. SAKAMAKO KAN TARIHI 6
II./.RUBUTU. 8
2.1. ALAMAR RUBUTUN FARKO.. 8
2.1.1/. RUBUTU SUMER. 8
2.1.2./. RUBUTU MAI LUNGU KO CUNEIFORME. 9
2.1.3./. RUBUTU NA HIEROGLYPHE. 10
2.2./. ALAMAR BABBAƘUN DUNIYA. 10
2.2.1./. BABBAKUN FARAR FATA. 10
2.2.2./. MA’ANAR BABBAƘUN A GIMILCE. 12
2.2.3./. BABBAƘUN BAƘAR FATA. 15
III./. A SAKE BINCIKE KAN RUBUTUN AINAHI 16
3.1./.AINAHI KO TUSHEN RUBUTUN HAUSA. 16
3..2./. ANFANINSA. 16
3..3./. ALAMAR RUBUTUN HAUSA. 16
3.4./. YANAYIN FURUCIN HAUSA. 16
3.5./. BABBAƘUN HAUSA. 16
3.5.1./. WASULLAN HAUSA. 17
3.5.2./. LANGAYEN WASULLAI 17
3.5.3../. GOYON WASULLAI 17
3.5.4./.AYOYI 17
3.5.5./. ƴAN LISSAFI 17
3.5.6./. WAKILLAN ƴAN LISSAFI 17
TAƘAITAWA. 18

RATAYE…………………………………………………………………………………………17

LITTATTAFAN BINCIKE……………………………………………………………………….17


AINAHIN HAUSA


GABATARWA

A’uzu billahi minal shaitani razim. Bismillahi Rahamani Rahim
Assalamu alaikum jama’a Yan uwa, kuma barkammu da yau.

Idan ba ku manta ba, yau da ‘yan shekaru ke nan, muka ce muku, harshen hausa, harshe ne na farko, wanda daga gare shi ne yawancin harsunan duniyar nan suka fita; kuma mun ƙara da cewa hausa na da rubutu, wanda shi ma ya aifi yawancin rubutu da yawancin mutane ke anfani da shi kamar su Latina, Larabci da sauransu. To, ina hujjar wannan bayani?

Za mu yi anfani da harshe da rubutun hausa, domin a gane. Sai ku biyo mu sau da ƙafa.

I. /. Harshen hausa

Tabbat, harshen hausa, harshen farko ne, kuma da izinin Allah, za mu gwada muku hujjojin. Yanzu dai za mu yi anfani kaɗan da harshen hausa don mu nuna muku kaɗan daga cikin martabobinsa.

Idan ba ku manta ba, ƙasa da rana da wata da tarmamu da saurensu, sun bayyana ne a gare mu, bayan tsayuwar jirgin tsira na Annabi Nuhu (T.A.A.T.G). A lokacin da rana da wata da tarmamu suka bayyana, wata ƙabila ta riƙa bauta musu, bauta ta fuskar addini. Kuma jagoran addinin shi ne wakilin rana da wata da tarmamu da saurensu.

To wace ƙabila ce ta farko wadda ta bauta ma waɗannan abubuwan? Ai babu shakka HAUSAWA ne !

Hujja ?

Sunaye da kalmomi kuma da karin magana dangane da rana da wata da tarmamu da saurensu da ake samu a cikin harshen hausa. Wakillan Rana da Dare, can da farko, RA da RE ake kiransu da hausar ainahi.

Ƙaƙa RA da RE za su ba mu kalmomi da sunaye da karin magana da yawa a cikin harshen hausa ?

RA da RE wakillan rana da dare ne, kuma su ne za su yaɗaɗa addini ko’ina cikin duniyar nan. Yaɗuwar addinin RA da RE (kowa da nashi), zai ƙarfafa harshen hausa ta fuskar kalmomi da sunaye da karin magana, kamar haka:
1.1. /. Da kalmar RA.
Za mu samu haka:
- RA - NAWA
- RA - NAW
- RA – NA

RANAWA, da RANAW da RANA, dukkansu ma’anarsu guda ce, cewa da ALLAH NE. To, masu sauraren mu, kar a zarge mu da cewa mun soki ra’ayin addinin musulunci ko na christa ko kuma can wani addini, muna bada wannan sanarwa, domin a san mafari da manufa. A game da wannan lamari na RA - NA, waɗanne kalmomi ne da sunaye da karin magana za mu samu?
A kwai :
- RANA
- RANI
- RANAU
- RAKEA
- RANARKA
- BA KA DA RANA
- RANKA YA DAƊE
- ds…

Idan an ji kuma an gane da yanda muka samu kalmomi da sunaye da karin magana da RA ko da RE, ƙaƙa ne? Wannan tambayar ce ke ba mu damar anfani da aji na biyu, cewa da RE.

1.2. /. DA KALMAR RE

A fuskar bauta ma rana da wata da tarmamu, ba a kiran RA ba tare da RE ba. Wannan al’amarin zai ba mu kalmomi, da sunaye da Karin magana kamar haka:
- RA – NAWA da RE
- RA – NAW da RE
- RA – NA da RE

Dukan waɗannan sheɗarun ma’anarsu guda ce, cewa da RANA DARE, inda muke ƙwanƙwance sunayen rana da dare, wa’anda suke makamman ainahi na awon lokaci ga harshen hausa. A game da RE waɗanne kalmomi da sunaye da Karin magana ne za mu samu?
A kwai:
- DARE
- ADARE
- BABARBARE
- BA’ADARE
- BA’ARE
- GARE KA
- RENI
- ds...
Kun dai ji a taƙaice, kuma kun gane da yanda muka samu kalmomi da sunaye da karin magana da waɗannan kalmomin cewa da RA da RE, waɗanda a duniyar nan, ba su da ma’ana in ba ga harshen hausa ba. Kuma idan ba ku yarda ba ku jarraba da duk harshen da kuke so, ku gani!
1.3. /. SAKAMAKO

Dangane da wannan sanarwa, mine ne ya kamata a gane kuma a riƙe?

Na ɗaya shi ne, yanda harshen hausa ke gudanar da al’amuransa.
Na biyu ko, ya shafi kaɗan daga cikin tarihin hausawa.
Sai ku biyo mu sau da ƙafa.
1.3.1. /. SAKAMAKO KAN HARSHE

Abin da ya kamata a gane na farko a game da harshen hausa shi ne, harshen hausa kamar ƙwame yake, ba harshe ba ne wanda ke buɗe kamar yawancin harsunan duniya;

Abu na biyu wanda ya kamata a gane, kuma a riƙe game da harshen hausa shi ne wannan haɗuwa, gamuwa, ɗoriya, ko kuma auren ƙaramin baƙi da babban baƙi, wanda ake kira gaɓa ko syllable a turance. Harshen hausa ne kaɗai zai bada fassara da ma’ana a kowace gaɓa;

Abu na ukku wanda ya kamata a gane shi ne lauɗi: ana iya a ja shi, ko a taƙure shi, ko kuma a lanƙwasa shi; wannan lauɗin na harshen hausa, ya ɗauko tushensa ne daga wannan ɗoriyar gaɓoɓin.

Wannan lauɗin na harshen hausa na ba mu damar kwatamta sheɗara ko jumla, kamar sarƙa, ita kuma gaɓa ko syllable kamar zobe. Ku san da sani cewa, idan a kwai zobe, to sarƙa ba ta ƙarewa, haka harshen hausa yake;

Abu na huɗu wanda ya kamata a gane ga harshen hausa shi ne: duka kalma, sheɗara ce ko jumla; haka kuma duka sheɗara ko jumla na iya taƙurewa ta koma kalma, kamar dai yanda kuka ji ɗazu.

Abu na biyar wanda ya kamata a riƙe shi ne bambanci da ke da kwai tsakanin harsunan duniya:

- Akwai harsuna na ainahi, kamar harshen hausa; Harshen ainahi kamar ƙwame yake, ba harshe ba ne wanda ke buɗe, a rufe yake, idan babu mabuɗi, sai a yi haƙuri.
- A kwai aifaffi; Su dai aifaffin harsuna, rabi rufe rabi buɗe; kuma ba su kama da ƙwame.
- A kwai yayayyi, waɗanda a buɗe suke samsamsam.

Abin da ya kamata a gane kuma a riƙe a nan shi ne, kwatamci da harshen hausa; duk harshen da ba ya yi kamar harshen hausa, to ba na ainahi ne ba, kuma ƙarshensa ɓacewa, ba yin mutum ba ne, sarautar Allah ce.

Kun dai ji a taƙaice kaɗan daga cikin al’amuran harshen hausa, yanzu sai mu shiga kaɗan daga cikin tarihin hausawa.

1.3.2./. SAKAMAKO KAN TARIHI

Sakamako na farko kan tarihi, shi ne tabbata muku da cewa, mutanen farko a duniyar nan, wanda suka fara addini, baƙaƙe ne, kuma hausawa ne; sun fara da addinin rana da wata da tarmamu, sai addinin gumaka ya biyo, sannan sauran;

Sakamako na biyu kan tarihi shi ne, maimaitawa da ƙwanƙwancewa bisa ga mutanen farko na ƙasar Misira ko Egypte.

Idan ba ku manta ba, Farfesa CHEICK ANTA DIOP (Allah ya jiƙan shi, amin) na ƙasar Sanagal, ya tabbata muna da cewa mutanen farko na ƙasar Misira, ainahi baƙaƙe ne, mu kuma muka ƙara da cewa hausawa ne. Ga hujjojin:

- Hujja ta ɗaya, hoto ne, da muka ɗauko cikin littafinsa mai suna baƙaƙe da al’adunsu, ko kuma NATIONS NEGRES ET CULTURES, bugu na huɗu, shafi na ɗari da goma. Shi dai wannan hoto an ɗauke shi ne kamar Fira’auna; Fira’auna ko kun san Misisra ce;
- Hujja ta biyu, ita ce MAGAJIYA RAKEA, wadda ke ta ukku cikin sarakunan Gobirawa, sanannu. Za mu ɗan dakatawa kaɗan bisa ga MAGAJIYA RAKEA domin ƙarin bayani.

Magajiya, kun san dai sarautar mata ce a ƙasashemmu na hausa? Kuma wakiliyar ‘yan bori ce!
Rakea ko suna ne na mata a ƙasashemmu na hausa.

Idan ba ku manta ba, mun shaida muku da cewa, harshen hausa, harshe ne mai kwaɗo, to za mu sa mabuɗi mu buɗe kwaɗon domin mu gane ma’anar wannan suna na RAKEA.

RAKEA suna ne mai nuhin RA-KE-A-EA. Kun gani a nan, sheɗara ce, ko jumla. Idan ta taƙure, ta koma suna, sai ta ba mu RAKEA.

EA, INNA dukansu ma’anarsu guda ce, cewa da uwar ‘yan bori.

A taƙaice RAKEA na nuhin uwar ‘yan bori. Wato MAGAJIYA.

Wannan maccen, cewa da MAGAJIYA RAKEA, ita ce gimbiya ta farko a duniyar nan, wadda ta kafa iko da addini a cikin ƙasar Misira.

- Hujja ta ukku, wannan sunan na Fira’auna, ko kuma FARAON, wanda ‘yan mulkin mallaka suka laƙa ma sarakunan Misira, kalmar hausa ce, kuma tana dangane da wannan gimbiyar, bahausa, cewa da RAKEA.

Abin ganewa a nan, shi ne can da ainahi FARAU a ke cewa; kuma FARAU na nuhin waɗanda suka fara kafa mulki da addini a cikin ƙasar ta Misira, da magadansu; idan kun yi la’akari, dukansu na da sunaye wanɗanda ake kiran su da shi.

Kenan al’amarin Fira’auna daga baya ne ya wanzu, zamanin ikon ‘yan mulkin malakka, inda suke kiran Sarkin Misira da wannan laƙabin.

- Hujja ta huɗu, rijiya ukku cikin ƙasa ukku; ko wace rijiya na game da ‘yar uwarta da sarƙa; rijiya ta farko na nan cikin Misira; biyu ɗin na nan cikin ƙasashen Afirka, baƙar fata.
- Sakamako na ukku kan tarihi shi ne gadon iko da addini na gargajiya gare mu hausawa.

Iko da addini na gargajiya, sun ɗauko tushensu ne daga RA da RE; kuma wannan kalma ce hujja: HATTARASA. Wanda duk ya je fadar sarakunammu na gargajiya ya ji wannan kalma; to minene ma’anar wannan kalmar? Za mu sa mabuɗi mu buɗe kalmar domin mu gane ma’ana ; sai ku biyo mu sau da ƙafa:

HATTARASA
HAR TA RA SA
HAL TA RA SA
HAG GA SARAUTA RA SA
HAR GA SARAUTA RA SA
HAL GA SARAUTAR RA SA
HATTARA SA!
Dukkan su ma’anarsu guda ce, cewa da hattarasa.

Kuma duka sarki na hausa da rawani aka san shi ; kenan rawani hikimar sarauta ce ; idan haka gaskiya ne to mine ne ma’anar rawani? A nan ma za mu yi anfani da mabuɗi domin fahimta ;
RAWANI kalma ce wadda ta ƙumshi gaɓa ukku :

A kwai RA (ku tuna da bayanin ɗazu),
a kwai WA (mai nuhin babba, magaji),
a kwai NI (aikau) mai nuhin mai magana.
Kun ga RAWANI kalma ce mai nuhin zawati ko kyalle na naɗawa ga kai, to amma idan muka walwale kalmar sai mu gane ma’ana da manufa. Kenan RAWANI al’adar hausawa ce, kuma ta ɗauko tushenta ne tun daga RA.

- Sakamako na huɗu, shi ne gadon sarautar mata ga hausawa. Tabbat, ikon Sarauniya SABA, Sarauniya DAURA, Sarauniya TAHAWWA, Sarauniya MANGOU, ba tatsinniya ba ce, gaskiya ne, kuma dukansu sun ɗauko tushensu ne daga RA.

- Sakamako na biyar shi ne jikokin waɗanda suka gina waɗannan daulolin na ƙasar Misira, waɗanda ake kira pyramide, na nan cikin Najeriya da Nijar.

- Sakamako na shidda, shi ne jikokin Nubiyawan farko, na nan cikin Najeriya da Nijar.

- Sakamako na bakwai shi ne yawancin sunayen ƙabiloli, hausa ce. Misali: SUMERIEN, AGADIEN, KANANEEN, ARAMEEN, MANDING, BAMBARA, KOTO KOLLI… ds.

- Yawancin sunayen ƙasashe, hausa ce. Misali: BABYLONIE, EGYPTE, HABASHA, SOMALIE, YEMEN, INDE …ds.

- Sakamako na takwas, shi ne ƙaryatar da tarihin hausa na banza bakwai da hausa bakwai.

- Sakamako na tara, shi ne ƙaryatar da ƙazafi da jahilci da ‘yan ƙar da ƙamzon kurege ke yi, cewa hausawa larabawa ne, ko kuma yawancin kalmomin hausa larabci ne.

Abin da ya kamata a gane shi ne, kafin Annabi Mohammadu (S.L.A.S) ya zo duniyar nan, har ya bayyana, akwai hausawa; kuma a san da sani cewa Annabi Mohammadu (S.L.A.S), annabi ne na ƙarshe sananne, kuma dalilin shi ne, harshe da addinin larabawa suka yaɗu, a lokacin nan tuni hausawa sun ƙaura.

Yaɗuwar addinin musulmunci, ko kuma jihadi da aka yi nan a ƙasashemmu na hausa, tsakanin junammu ne, baƙaƙe ; kuma yawancin mayaƙan ba su jin larabci, balle a ce an ci mu da yaƙi, kuma an bida mu da harshen larabci.

Akwai abu guda wanda lalle mun yi imani da shi, shi ne aro, ko kuma fanfaɗe da ke akwai tsakanin harshe da harshe, idan sun haɗu wuri guda.

To a faɗa muna inda hausawa suka zamna tare da larabawa a nan Afirka, har harsunansu suka shiga juna, inda hausa ta gaɓɓato, ko kuma ta zaɓɓato kalmomin larabci?

Haba jama’a, kar mu zama ‘yan amshin shata, ko kuma kwando abin zuba shara. Mu hankalta, mu nazarta, mu ƙwanƙwanta, mu maida niyya ga bincike domin fitar da takaici da jahilci, domin cin gaban kammu da kammu.

Da wannan gargadi muke dasa aya ga wannan babi, sai kuma mu gyara zama, mu karkaɗe kunnuwammu, domin sauraren babi na biyu, wanda ke ba mu bayani kan rubutun hausa, inda nan ma, za ku ji hikimar kakannimmu.
II./.RUBUTU
2.1. ALAMAR RUBUTUN FARKO
2.1.1/. RUBUTU SUMER

Rubutun farko a duniyar nan sananne, an same shi a cikin wata ƙasa wadda a ke kira MESOPOTAMIE, musamman ma a SUMMER.
(projection)

MESOPOTAMIE, kalmar Girkawa ce mai ma’ana MESOS (tsakkiya) POTAMOS (ruwa), wanda muke kira tsibiri da harshen hausa; tsibiri ko kalma ce wadda ta fito daga cibi RA; cibi RA na nufin wuri inda rana ta fara bayyana a cikin duniyar nan.

SUMMER ko, fassarar kalma ce mai faɗin daga inda masu rubutun suka fito. Sumer ko kalmar hausa ce mai nuhin bisa.

Ga wani dan misali, domin ku gane al’amarin:

- DU ga wannan kalmar an yi hoton tudu;
- SAG ga wannan an yi hoton kai tsaye;
- DU ga wannan an yi hoton tafiya ko gudu;
- KUR ga wannan an yi hoton duwatsu;
- TUM an ce ɗauka;
- DUDU an ce ƙafa, dudduge;
- GUB an ce tashi tsaye, ko kuma sa ;
- KI. an ce kibbiya ko kuma kihi.

Dukan waɗannan kalmomin, ba su da ma’ana ga larabci ko ga yahudanci, ko kuma ga duk harshen da kuke so, in ba harshen hausa ba; ku tuna da abin da muka shaida muku ɗazu. Don dai ku gane, kuma ku yarda, za mu shiga cikin ma’anar wannan kalmomin. Sai mu koma ga ma’ana ta sama.
2.1.2./. RUBUTU MAI LUNGU KO CUNEIFORME

Shi dai wannan rubutun ana kiran shi da sunan «écriture cunéiforme» ; wannan kalmar ta CUNEIFORME ta fito ne daga CUENUS mais nufin lungu, FORME (kama) ; a taƙaice dai wannan kalmar na nufin rubutu mai lunguna ko kuma mai kama da ƙusa ;

Ga dai alamar rubutun:
(projection)

Abin tambaya a nan shi ne: wace ƙabila ce ta ƙirƙiro wannan rubutun?

Masu ilimin bincike, sun faɗi cewa, wannan hikimar SEMITES ce, wato Yahudawa da Larabawa da saurensu, tunda su ne aka tarda a wurin. Amma inda abin yake da ɗarmun kai, shi ne yanda su magadan rubutun, ba su anfani da shi ta fuskar ƙere-ƙere ko sutura ko gini ko lamba ko shaidu…ds, har su bada gudummuwa ga ƙwanƙwancewa da fassarar rubutun .

Wannan lamarin ya ɗaure ma yawancin masu ilimin harshe kai, ko kuma masu nazari. Wannan hanyar da suka ɗauka, ba ta dace ba , shi ya sa waɗansu masu hankali, kamar Jean BOTTERO, sun yi watsi da lamarin, inda suka ce ya kamata a maida bincike bisa ga wasu ƙabilu inda waɗannan kalmomin za su samu ma’ana cikakka. Wannan daidaituwar, za ta bunƙasa, kuma za ta ƙarfafa wannan ilimin da ake kira archeologie, wato (ilimin kufai).

A fuskar rubutun, gogayen aikin sune :

Ø SIR WILLIAM FLINDERS PETRIE (1905);
Ø A.H.GARDINER, (1915);
Ø ALBRIGHT, (1948);
Ø CLAUDE SCHAEFFER; (1929)…ds.

A nan, sakamako ya rinjaya ne ga yanda mutanen ke anfani da laka ta fuskar rubutu, ko kayan aiki ko na ƙawa da saurensu. Waɗannan abubuwan namu ne, tunda har kwanan gobe, za mu yi anfani da su. Akwai wasu abubuwa waɗanda aka binciko a nan ƙasashemmu na Afirka masu kama da hakanan. Idan ko haka gaskiya ne, to biri ya yi kama da mutum.

A cikin wani littafi mai suna « tsakanin adali da rubutu , shekara ta 1994» da malam JACK GOODIE ya gabatar, mun samu wurin da aka ba mu bayani kan wannan rubutun, cewa ya ƙumshi babbaƙu talatin da biyu (32). Su dai waɗannan babbaƙun ana rubuta su ne daga hauni zuwa dama, kuma sun fito ne daga cikin na Kanana ainahi tun ƙarni goma sha hudu kahin aihuwar annabi ISA (T.A.T.A.).

Shi kuma wannan rubutun ya aifar da na PHENICIENS, mai babbaƙu ishirin da biyu (22) ; su kuma Yahudawa da Girkawa, sun ramta daga gare su wajen ƙarni goma sha ukku.

2.1.3./. RUBUTU HIEROGLYPHE

Idan kuma mun komo ga wannan rubutun HIEROGLYPHE, wato HIERO (sacre: tsarkakke) GLYPHE (écriture: rubutu), sai mu gane da cewa duk waɗannan kalmomin, na harshen Girkawa ne, ke nan rubutu ya rinjaye su; Idan ko haka gaskiya ne, abun tambaya a nan shi ne: shin wai su masu yin wannan rubutu, farfaru ne ko baƙaƙe? Ƙaƙa suke kiran rubutun? Ba a yin la’akari da wannan damuwar, sai dai a cilasta muna da ƙarya.

Ba za mu yarda ba, kuma da iznin Allah za mu ci gaba da bincike don ci-gaban kammu da kammu.
2.2./. ALAMAR BABBAƘUN DUNIYA

Alamar babbaƙun duniya ta kasu gida biyu : akwai na farar fata, kuma akwai na baƙar fata.

2.2.1./. BABBAƘUN FARAR FATA

2.2.1.1./. EGYPTE

A. I. Y. Y. W. W. B. H. P. F. M. M. N. R. H. H. H. H. S. S. CH. K. K.F. G. T. TJ. D. DJ.

(projection)
2.2.1.2./.COPHTE

A. V. G. D. E. S. Z. I. TH. I. K. L. M. N. X. O. P. R. S. T. E. F. CH. PF. O. SC. F. CH. H. G. SC. D.

(Projection)

2.2.1.3./. GREC

Babbaƙun grec sun kasu gida ishirin da huɗu (24); ga yanda suke:
A .V.G. D. E. Z. I.TH. I. K. L. M. N. X. O. P. R. S. T. Y. PH. CH. PS. O.

Idan muka lura, a cikin babbaƙun, babu waɗansu, kamar su B. C. F. G. H. J. Q. U. W.Y.

(projection)

A game da ainahin waɗannan babbaƙun, ra’ayi ya kasu gida biyu:

Ø Waɗansu kamar GELB sun ce an ƙirƙiro su a Grece wajen 750 kahin aifuwar Annabi ISA;
Ø Waɗansu ko sun ce Samidawan yamma ne suka ƙirƙiro su wajen 700 kahin aifuwar Annabi ISA.

A game da babbaƙun, abin da Girkawa suka yi, shi ne ƙara hikima ga wasulla daidai da harshensu.

Idan muka dawo kan babbaƙun, za mu gane da cewa, Girkawa da Samidawa sun yi abun ga da hausawa ke cewa “hankaka maida ƙwan wani naka”. Waɗansu masu hankali, kamar su COLDSTREAM 1977, HAVELOCK 1973, GOODY da WATT 1963, sun ce wannan zance bai dace ba; Inda rubutu ya fito ainahi, shi ne ASIE MINEURE. Sun ƙara da cewa babbaƙu da tsari da kamar babbaƙu, aikin mutane ne masu magana da harshen KANANA, harshen Samidawa.

Kash! Ga zance ya bi hanya to amma sai ya ratse, tunda cikin sarakunan gobirawa sanannu, akwai na farin mai suna KANANA, Gobirawa ko baƙaƙe ne. Idan ko haka gaskiya ne, Kananawa ba Samidawa ba ne, ba Larabawa ba ne, ba Yahudawa ba ne, ba Geze ba ne, ba ma Kiyaya ba ne , manoma ne, kuma suna cikin zuri’ar jikokin Annabi Nuhu (T. A..A.S.T.G.).

2.2.1.4./. LATINA
A. B. G. D. E. V. Z. K. L. M. N. O. R. T.
(projection)

2.2.1.5./. YAHUDAWA

Babbaƙun Yahudawa talatin da ɗaya ne; ga dai kamanninsu:

A. B. V. G. D. H. W. Z. H. T. Y. K. KH. K. L. M. M. N. N. S. A’. P. F. F. TS. TS. K. F. SH. S. T.
(projection)
2.2.1.6./. LARABAWA
A. B. T. TS. DJ. H. KH. D. Z. R. Z. S. SH. S. DH. T. Z. A’. GH. F. Q. K. L. M. N. H. W. Y.
(projection)

2.2.1.7./. ETHIOPIE

H. I. H. M. S. R. S. S. Q. B. T. TCH. H. N. GN. A. K. H. W. A. Z. S. Y. D. J. G. T. TCH. P. S. S. F. P.
(projection)

2.2.1.8./.LYBIQUE
B. G. D. W. Z. Z. Z. T. I. K. L. M. N. S. S. F. C. Q. R. S. T. T.
(projection)

2.2.1.9./. TIFINAGH

B. CH. D. D. F. G. DJ. H. I. J. K. O. KH. L. M . N. W. R. S. T. T. Z.
B. G. D. H. W. Z. H. T. Y. K. L. M. N. S. G. S. Q. R. S. T. F. G. Z. D. D. Z. H.
° = a; é; e; i
(projection)


Abin da ya kamata a lura da shi a nan, shi ne yanda babbaƙun suke:
Ø zube barkatai;
Ø ba tsari;
Ø ba ma’ana;
Ø ba a san ba wanda ya ƙirƙiro su;
Ø waɗansu sun fi waɗansu yawa ;
Ø babu cikakkun wasullai ;
Ø babu ayoyi
Ø babu langayen wasullai ;…ds.

Ko wannan al’amarin ne ya sa, watakila, ake kiran rubutun zamani da sunan « écriture conventionnelle : rubutu na yarjejeniya » ?

2.2.2./. MA’ANAR BABBAƘUN A JIMILCE

ALEPH na nufin “sa” da harshen semitique, wannan baƙi babu shi ga harshen Girkawa, amma sun ɗauke shi kamar «a» ;

BET: na nufin “gida” ko “tanti”, kuma ma’anar shi “b”;

GAML: na nufin “raƙumi”, ko kuma “tozon raƙumi” g;

DELT: na nufin “ƙofa” d;

HE: babu ma’ana h;

WAU : na nufin “kusa” ko kuma “ijiyar sau”; babu shi da harshen Girkawa:

ZAI : na nufin “icce mai bada olive”;

HET: na nufin « katanga » ko «shimge» ;

TET : babu ma’ana ;

YOD : na nufin « hannu » ;

KAF: na nufin « tahin hannu » ;

LAMD: babu ma’ana;

MEM: na nufin “ruwa”;

NUN : na nuhin “kihi”;

AIN: na nufin “ijiya”;

PE : na nufin “baki”;

SADE :na nufin “ɗan fatsa” ko “lauje” ko kuma “hanci”;

QOF: babu ma’ana;

RES: na nufin “kai”;

SIN : na nufin “haƙori”;

TAU : na nufin “shaida” ko kuma “lamba”.

Idan aka jimilta waɗannan babbaƙun, sai mu ce su ishirin da ɗaya ne (21); waɗansu na da ma’ana, kuma waɗansu ba su da ma’ana;

Abin da muka gane a nan , shi ne: harsuna ukku ke anfani da waɗannan babbaƙun: akwai yahudanci, akwai larabci, akwai misiranci. Misiranci ko ba harshen semites ba ne, kamar yanda ake kirari cewa babbaƙu ko kuma alphabet aikin Samidawa ne. Abun tambaya a nan shi ne, yaya ake ƙera abun da ba ya da suna, ba ya da ma’ana?

A nan ma, ya isa mu gane da cewa, alphabet dai, ba aikin Samidawa ne ba, kuma ba aikin Turawa ne ba; idan haka gaskiya ne, to ina ya kamata mu maida bincike da nazari kan asalin rubutu, ko kuma asalin alphabet ?

Tunda su dai Shinuwa (mutanen Sin) da Indiya (mutanen Hindu) ba su da alphabet, ai sai mu nuho Afirka, baƙar fata, mu gani ko!

To haka ɗin ba ta faru ba; ke nan dai, sun sani, don wannan ne, ta wani fanni, ake gallaza muna, ake sa muna yunwa da ƙishirwa, da yaƙi da sauransu, don kar mu ci gaba! Abun tambaya a nan shi ne : shin wai wannan rubutun da su Turawa da Larabawa da sauransu ke tamaƙa da kuri da shi, daga ina ya fito ? To a nan ne babbar hikimar wannan sakamakon bincikemmu da nazari kan rubutun hausa da za mu ba ku zuwa gaba idan Allah Sarkin sarauta ya yarda.

Kafin ranar za mu ba ku ɗan bayani kaɗan ga ma’ana da fassara kan babbaƙun latina ko na larabci, kamar dai yanda Turawa masu bincike da nazari kan lamarin suka faɗi ; Ga wani ɗan misali wanda LOUIS-JEAN CALVET, Farfesa na ilimin al’umma da harshe na Jami’ar SORBONE ya bada a cikin littafinsa mai suna « HISTOIRE DE L’ECRITURE : Tarihin Rubutu», FEVRIER 1997:

Idan muka gane da cewa baƙi ya fito daga hoton abubuwa, to a nan ma, waɗansu babbaƙun, ba su da tushe; yaya aka yi haka? Zancen ga ko akwai gaskiya dai? Idan muka ɗauki ɗan misali kaɗan kan babbaƙun (aleph da delt), sai mu ce akwai duhu cikin lamarin;

Kowa ya san Larabawa da Yahudawa ba makiyayan shanu ne ba; ba su da shanu duk duk duk; To daga ina ne “sa” ya fito har yake nufin “a”?

To amma inda wannan lamari zai fi dacewa, da inda zai fi ma’ana sai ga HAUSAWA (masu hawan shanu); wanda ko ba ya da sa, ba shi hawan sa, balle ya yi zancen sa! Ke nan wannan baƙi, cewa da A, tushen alphabet, magana ce a dunƙule, mai nufin masu shanu mafarin alphabet, biri ko ya yi kama da mutun; za ku samu ƙarin haske zuwa gaba, bayan exposition (nuni) da iznin Allah !

Baƙi na biyu wanda muka ɗauka don misali, shi ne DELT; shi dai wannan baƙin an ɗauke shi kamar ƙofa mai lungu ukku. Abun tambaya a nan shi ne: wane irin gida ne mai wannan ƙofar, wanda ya dace da tabi’o’in makiyaya, masu gidan fata? Wannan ma’ana dai ba ta dace ba, kuma haka dai ake yi domin a ɓatar da mu, a ƙara tura mu cikin daji.

Kun ji kuma kun gani, yanda ake horon mu da cewa rubutu, aikin makiyaya ne, musanman Larabawa da Yahudawa. Akwai gaskiya ko ? Amsa na gare ku matasa.

Abin da muka amince ma, shi ne yanda babbaƙu ke fitowa daga hoto; amma fassara da ma’ana da tushen babbaƙu na latina da na larabawa da yahudawa, ba mu amince ba, kuma za mu yi yaƙi matuƙa kan lamarin har gaskiya ta tabbata da iznin Allah !

Ga dai wani ɗan misali tamkar shirme wanda shi wannan baturen, Farfesa CALVET, ya rubuta kan ainahin baƙi.

(projection)

Na ɗaya, ya ɗauki hoton rana, wanda ake kira da sunan “soleil” da harshen faransanci, “solej” da wani harshe.

Na biyu, ya ɗauki hoton rana, wanda ake kira “ra” da harshen mutanen Misira, wanda ya kira copte, “soleil” da harshen faransanci. Sai ya ce waɗannan misalan biyu, ba su da dangantaka, kuma ba su kama da juna ta fuskar ainahin baƙi.

Wacce ce hujjarsa, tunda ya ce wannan kalmar ta mutanen Misira ce, ai akwai su can dauri, ya tambaye su mana, ya ji ma’ana ko kuma fassarar “ra”, in dai har binciken gaskiya ne yake yi, ai zai gane kurensa, domin ƙarin haske kan lamarin, to hakanan ɗin ba ta faru ba, don son rai, don son suna da girman kai.

Akwai dangantaka ƙwarai tsakanin misalan biyu, kuma suna kama da juna ta fuskar ainahin baƙin. Idan ba ku manta ba, ai “ra” rana ce ko, kuma mun gani yanda wannan kalmar ta “ra” ta ba mu kalmomi, da sunaye da karin magana a cikin harshen hausa; Kuma harshen hausa kaɗai ya kai hakanan, wanda duk ya yi gardama ya jarraba ya gani.

2.2.3./. BABBAƘUN BAƘAR FATA

A game da rubutun duniya, Turawa sun ce, kowace ƙabila ta gwada hikimarta kan lamarin ; To amma shi baƙin mutum, iliminsa bai ba shi wannan fusa’ar ba ; Wannan ƙazafi ya damu wasu Afirkawa, inda suka ƙirƙiro rubutu iri-iri, kamar haka:

(projection).

2.2.3.1/. WOLOF

A. C. M. K. B. MB. J. NJ. S. W. L. G. NG. N. D. ND. X. H. Y. T. R. N. F. N. R.

2.2.3.2./. MASABA

P. T. C. K. B. D. J. G. F. S. NZ. M. N. NY. N. Y. W. H. L. R.

2.2.3.3./. MANENKA

H. P. R. DY. TY. D. R. S. GB. F. K. L. M. NY. N. H. W. Y.

Abun takaici a nan , shi ne duk da kishin da waɗannan Afirkawa suka yi, rubutun nasu bai samu martaba ba kuma bai samu karɓuwa ba ga ma’ikontammu da mutane.

A game da ainahin babbaƙu da ma’anarsu, mun gano da cewa zama dai bai same mu ba, don haka muke cewa a sake bincike.
III./. A SAKE BINCIKE KAN RUBUTUN AINAHI
3.1./.AINAHI KO TUSHEN RUBUTUN HAUSA

Shi dai wannan rubutun, mun same shi ne ga wani bawan Allah, a jahar MARADI, ƙaramar hukumar Dakoro, jamhuriyar Nijar.

Wannan bawan Allah, bahaushe ne, bagobiri; Sunansa DOGUWA MAI WASA (Allah ya jiƙan shi. Amin). Manomi ne, kuma mahalbi ne. Ya gadi wannan rubutun ga kakansa, shi kuma ya hori jikansa mai suna ADARE SALIHU. Shi kuma Adare Salihu ƙane ne gare ni.
3..2./. ANFANINSA

Ana anfani da wannan rubutun ta fuskar bambanta magungunan gargajiya.

3..3./. ALAMAR RUBUTUN HAUSA

Babu shakka hausawa na da rubutu, wanda ke ƙumshe da ma’ana, da hikima, da ƙayatarwa.
Ga alamar rubutun:
(Projection)

Rubutun hausa na ƙumshe da abubuwa guda biyar masu ɗimbin ma’ana:
3.4./. YANAYIN FURUCIN HAUSA

Kafin mu ba ku bayani dalla dalla, muna son mu fara da yanayin furuci na harshen hausa.
Harshen hausa na da yanayin furuci guda goma sha ɗaya (11):
- Akwai zuzau
- Akwai tunkuɗau
- Akwai ragaɗe
- Akwai ragare
- Akwai tsayau
- ds…
3.5./. BABBAƘUN HAUSA

Idan ana son a jimilta babbaƙun hausa, sai mu ce su arba’in da ɗaya ne (41). Yaya ne su babbaƙun ke gudanar da rayuwarsu ? Sai ku saurare mu da kyau.

Babbaƙun hausa sun kasu gida biyu :
- Akwai maza ;
- Akwai mata ;
- Akwai manya ;
- Akwai ƙanana.

Idan kuma muna son mu kwatamta babbaƙun hausa, sai mu ce al’amuransu ɗaya suke da duk halittar Allah. Tunda mun shaida muku da cewa a cikin babbaƙun hausa akwai maza kuma akwai mata, to ku san da sani aure zai wanzuwa tsakaninsu, inda a cikin arba’in da ɗaya, takwas aifaffi ne. Wannan lamarin na babbaƙun hausa, zai ba mu damar ganewa da wannan hikimar ta bambanta namijin kalma da tamatan kalma (wanda ake kira a turanci genre), tunda kalmomin da babbaƙu aka yi su; Wannan wani abun ƙayatarwa ne ga masu ilimin harshe, inda har yanzu ba su hango ba da cewa a cikin babbaƙu, akwai maza kuma akwai mata. Dukansu babbaƙun, kowanne da sunansa, kuma da ma’anarsa.

3.5.1./. WASULLAN HAUSA

Bayan babbaƙun hausa, akwai wasulla. Dukan tursassan wasullan hausa su bakwai ne (7); Kowane wasali da sunansa kuma da ma’anarsa.

3.5.2./. LANGAYEN WASULLAI

Alamar rubutun hausa ta ukku, ita ce langayen wasullai. Su ma sun kasu gida bakwai; a cikinsu akwai masu tafiya da manyan babbaƙu, kuma akwai masu tafiya da ƙananan babbaƙu. A nan ma, kowane langayen wasali da sunansa da ma’anarsa, kuma da aikin da yake yi bisa ga kowane baƙi.

3.5.3../. GOYON WASULLAI

Akwai goyon wasullai, su ma su tara ne (9). Akwai ‘yan biyu, akwai ‘yan ukku, akwai ‘yan huɗu.

3.5.4./.AYOYI

Alama ta huɗu ita ce ayoyin hausa. Ayoyin rubutun hausa sun kasu gida goma (10), kuma kowace aya na da sunanta da ma’anarta, da aikin da take yi a kan kowace sheɗara ko jumla.

3.5.5./. ‘YAN LISSAFI

Alama ta ƙarshe ita ce ta ‘yan lissafi, su kuma sun daidata kan gida tara (9). Kowane ɗan lissafi na da sunansa da ma’anarsa.

3.5.6./. WAKILLAN ‘YAN LISSAFI

Wakillan ‘yan lissafin Hausa kala biyar ne (5): akwai ‘yan ragau, akwai ‘yan ƙarau, akwai ‘yan ruɓanyau, akwai ‘yan raɓau, akwai ‘yan daidaitau.

TAƘAITAWA
Ga wata tambaya, jama’a: shin wanda bai san ba daga inda ya fito, ƙaƙa za ya sanin kansa, har ya san manufa, har ya yi zancen wani? Saboda haka, dangi ‘yan uwa, muna kira gare ku: mu farka, mu tashi tsaye, mu so junammu, mu rungumi junammu, mu haɗa kanummu, mu yaƙi jahilci da talauci da sauransu, domin ci-gabammu da kammu, domin rayuwarmu da kammu, domin tsirar kammu da kammu.

A nan za mu dasa aya kan rubutun hausa, sauran bayani sai ranar bikin nuna ma duniya rubutun (exposition).





































BIBLIOGRAPHIE

1/.LA BIBLE

2/. BOUBOU HAMA, «Histoire du Gobir et de Sokoto», Présence Africaine, 1967

3/. C HARLES HOUGOUGNET «L’écriture», édition PUF

4/. CLAIRE LALOUETTE, «Au royaume d’égypte, le temps des rois-dieux», éd. Fayard 1991.

5/. CHAICK ANTA DIOP, «nations nègres et cultures», Présence Africaine, 1979

6/. CHAICK ANTA DIOP, « L’unité culturelle de l’Afrique noire », Presence Africaine, 1982

7/. CHAICK ANTA DIOP, «Parenté génétique de l’égyptien pharaonique et des langues négro africaines», NEA, 1977

8/. DOMINIQUE SOURDEL, «Histoire des arabes», Que-Sais-Je, PUF, 1985

9/. GEORGES ROUX «La mésopotamie», Seuil, 1995

10/. GERARD NAHON, «Les Hebreux», édition seuil

11/. JACK GOODY «Entre l’oralité et l’écriture», PUF, Juin 1994

12/. JEAN BOTTERO et MARIE JOSEPH STEVE «Il était une fois la mésopotamie», édition découvertes Gallimard, 1993.

13/. JEAN DORESSE, «L’empire du Pretre Jean, l’éthiopie antique», édition plon, 1957

14/. LOUIS JEAN- CALVET «L’histoire de l’écriture»,Plon, 1996.

15/. FRANCIS AUFRAY, «Les anciens éthiopiens», édition Armand Colin, Paris 1990

16/. LE SAINT CORAN

17/. HIRA DA :

KORAU ANGO;
DOGUWA MAI WASSA;
ADARE SALIHU.

21 comments:

  1. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Sannu Kowa,
      Sunana Mista, Rugare Sim. Ina zaune a Holland kuma ni mai farin ciki ne yau? kuma na gaya wa kaina cewa duk wani mai ba da bashi wanda zai tseratar da ni da iyalina daga mummunan halinmu, zan koma ga duk mutumin da ke neman bashi a kansa, ya ba ni farin ciki a gare ni da iyalina, na kasance ina buƙatar aro na € 300,000.00 don fara rayuwata gaba daya kamar ni uba daya ne da yara 2 Na hadu da wannan mai gaskiya kuma Allah yana tsoron mai bada rancen da zai taimake ni da rancen € 300,000.00, shi mutum ne mai tsoron Allah, idan kana bukatar aro Kuma za ku biya bashin don Allah ku kira shi ku gaya masa cewa (Mr, Rugare Sim) yana nuna muku shi. Tuntuɓi Mista, Mohamed Careen ta imel: (arabloanfirmserves@gmail.com)


      MAGANAR BAYANIN AIKIN LATSA
      Sunan rana......
      Suna na tsakiya .....
      2) Jinsi: .........
      3) Bukatar Lamuni: .........
      4) Tsawon Lamuni: .........
      5) Kasa: .........
      6) Adireshin Gida: .........
      7) Lambar Waya: .........
      8) Adireshin Imel ..........
      9) Gashi na wata-wata: …………… ..
      10) Aiki: ...........................
      11) Wanne rukunin yanar gizo kuka kasance game da shi …………… ..
      Godiya da kuma mafi kyawun gaisuwa.
      Email arabloanfirmserves@gmail.com

      Delete
    2. Alhamdulillah mash'Allah gaskiya muna matukar godiya da wannan kokarin naku Allah ya kara lafiya da karfin ilimi Amma don ALLAH abinda muke matukar bukata a yanzu shine
      Ayi kokari a gabatarda wannan rubutun na harshen Hausa domin mu koyeshi tun lokaci bai kure mana ba
      Sabida halin rayuwa idan yau kuna nan wataqila gobe babu ku Allah ya daukaka harshen Hausa Aamin

      Delete
  2. Allah Ya taimake mu Ya kuma kara inganta mana Hausar mu. Ameen

    ReplyDelete
  3. Rubutunku bai gamsar da ni ba, sannan kuma akwai kurakurai birjik a cikinsa, sannan kuma kun yi anfani da Hausar da ba karbabbiya ba mara adadi a rubutun naku, amma duk da haka ba za a ce ba ku yi kokari ba

    ReplyDelete
  4. Assalamualaikum.Da fatan Allah ya kara basira.Bana mamaki ko kadan da gano harrufan Hausa na asali.Domin kuwa tun 1998 nagano cewa Hausawa suna da kyakkyawar alaka da Harshen Nubiyawan Misira wadanda littafan Sheikh Anta Diop (African Origin of civilization,myth or reality da Civilization or Barbarism),suka tabbatar cewa bakakene.Kuma a lokacin da na zauna a Amurka,a 1998-2000,Dr Abdul na Temple University dake Philadelphia,PA,USA,(Allah ya Shiryeshi don ya dawo hanya),ya nuna min kalmomi guda goma wadanda yanda suke a harshen Firaunawan Misira haka suke a cikin harshen Hausa! Misali - Kashi da Rana da sauransu.......A karshe ina mai zaburar da Hausawa da mu dage da bincike da nazari wajen inganta harshenmu da al'adunmu , kuma atafarkin addininmu na musulunci.Mu gaggauta fassara ilimin zamani zuwa harshen Hausa don karantarda yayanmu da yarenmmu.Bayan na koyi yarurruka 5 kuma na ziyarci kasashe kusan 20,na shekara kusan goma a Rasha da Amerika,na gano cewa muna wahalar da kanmune kawai.
    Idan har munaso mu kafa tamu Daular me wayayyen kai(our civilization) ,wanda sauran Afirkawa da Bakake zasuyi Alfahari da koyi dasu,akan tafarkin Musulunci,to tilas sai munyi amfani da RUBUTUNMU da kuma HARSHEN HAUSA wajen karantarda yayanmu.Donme zamu ce sai munyi karatu da yaren wani.Mun mayarda yayanmu dakikai kawai don basa jin harshen Turawa!Bayan kuma India da Chana dama japan da larabawa duk da yaransu kuma da Rubutunsu suke karatu.Kuma ayau sunada Farfesoshi da basa jin turanci!Kuma har mejankunne yana rububin siyan hajarsu da fasaharsu da suka kera,ana zuwa makarantunsu da asibitocinsu daga Amurka da turai da sauran kasashen Duniya.A sannanne duniya zataga kimarmu kuma ta darajtamu kuma a sauraremu a matsayin yaya ingantattu.Balallene a somuba,amma wannan zai sa a mutuntamu kuma asayi hajarmu -kar abarmu abaya.Anan shugabanninmu da mu mabiya , babban aiki ya samemu.Inba hakaba, harsunan Turanci,Faransanci da larabci zasu hadiye Hausa tsundum suyi gyatsa, harma su nemi kari da makwabtanmu dake zaune kara zube kamarmu.Allah ya taimakemu.Amin.Dr Salisu Muhammad Arafat,NOH,Dala,Kano,Nigeria.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Allahumma Aamin gaskiya muna matukar farin ciki da wannan kokarin naku
      Kuma inch'Allahu zamu mai da hankali
      Amma don ALLAH abinda ya kamata a yi
      A wannan lokacin Shi ne a yi kokarin
      Bayyana mana rubutun wannan yaren na hausa domin mu koyeshi tun lokaci bai kure mana ba sai bida halin rayuwa

      Delete
  5. Nazarin Hausa Yana Matukar Burgeni, Harshen Hausa Tana Kumshe Da Dukkan Abubuwan Rayuwa Kuma Masu Tsarki, Idan Muka Ci Gaba Da Farfado Da Harshen Hausa Kuma Muka Yadashi A Duniya Kamar Yadda Ya Dace Kuma Akan Tsari, Hakan Ne Ma Yasa Nakeson Zama Babban Marubuci Saboda Na Yada Harshen Hausa,

    ReplyDelete
  6. ALLAH YA KARA BASIRA. AMMA MENENE ASALI DA KUMA TARIHIN KAN'ANA?

    ReplyDelete
  7. gaskiya naji dadin wannan bayani.a matsayina na mai nazarin harshen hausa.Allah ya amfanar damu da abunda maka ji.

    ReplyDelete
  8. Sunana Mashud Gordic. Ina zuwa kan layi kuma na sami bankin JOSE Luse wanda aka buga a cikin littafin wanda ya ce kamfanin aro ya ba wa jama'a yawan aro a wani ɗan ƙaramin saƙo.
    Don haka, na tuntuɓi kamfanin ta hanyar imel ɗinmu: joseluisloans@gmail.com
    wanda na nemi bashin $ 15,000 na tsawon shekaru 2. Kamfanin ya amsa min kuma ya aiko min da dukkan sharuddan kamfanin sa wanda na karanta kuma na yarda da su. Bayan amincewa da aikace-aikacen aro na, na samu sanarwa daga banki na cewa asusun banki na $ 15,000 ya kasance mai canzawa zuwa rupee, na gama biyan bashin a ranar 18 ga Disamba kafin fara fashewar corona.
    Don haka, zan so in yi amfani da wannan damar in aika sako ga duk wanda ke neman amintaccen mai ba da bashi na Intanet don neman lamunin jose luis ta hanyar e-mail: Account (joseluisloans@gmail.com)
    Hakanan zaku iya tuntuɓar su akan aikace-aikacen Menene: (+1 3075431042)

    ReplyDelete
  9. Sunana Mashud Gordic. Ina zuwa kan layi kuma na sami bankin JOSE Luse wanda aka buga a cikin littafin wanda ya ce kamfanin aro ya ba wa jama'a yawan aro a wani ɗan ƙaramin saƙo.
    Don haka, na tuntuɓi kamfanin ta hanyar imel ɗinmu: joseluisloans@gmail.com
    wanda na nemi bashin $ 15,000 na tsawon shekaru 2. Kamfanin ya amsa min kuma ya aiko min da dukkan sharuddan kamfanin sa wanda na karanta kuma na yarda da su. Bayan amincewa da aikace-aikacen aro na, na samu sanarwa daga banki na cewa asusun banki na $ 15,000 ya kasance mai canzawa zuwa rupee, na gama biyan bashin a ranar 18 ga Disamba kafin fara fashewar corona.
    Don haka, zan so in yi amfani da wannan damar in aika sako ga duk wanda ke neman amintaccen mai ba da bashi na Intanet don neman lamunin jose luis ta hanyar e-mail: Account (joseluisloans@gmail.com)
    haka nan za ku iya tuntuɓar su a cikin Aikace-aikacen Menene: (+1 3075431042) \



    aro

    ReplyDelete
  10. Halo semuanya, Nama saya Siska wibowo saya tinggal di Surabaya di Indonesia, saya seorang mahasiswa, saya ingin menggunakan kesempatan ini untuk mengingatkan semua pencari pinjaman untuk sangat berhati-hati karena ada banyak perusahaan pinjaman penipuan dan kejahatan di sini di internet , Sampai saya melihat posting Bapak Suryanto tentang Nyonya Esther Patrick dan saya menghubunginya melalui email: (estherpatrick83@gmail.com)

    Beberapa bulan yang lalu, saya putus asa untuk membantu biaya sekolah dan proyek saya tetapi tidak ada yang membantu dan ayah saya hanya dapat memperbaiki beberapa hal yang bahkan tidak cukup, jadi saya mencari pinjaman online tetapi scammed.

    Saya hampir tidak menyerah sampai saya mencari saran dari teman saya Pak Suryanto memanggil saya pemberi pinjaman yang sangat andal yang meminjamkan dengan pinjaman tanpa jaminan sebesar Rp200.000.000 dalam waktu kurang dari 24 jam tanpa tekanan atau tekanan dengan tingkat bunga rendah 2 %. Saya sangat terkejut ketika saya memeriksa rekening bank saya dan menemukan bahwa nomor saya diterapkan langsung ditransfer ke rekening bank saya tanpa penundaan atau kekecewaan, segera saya menghubungi ibu melalui (estherpatrick83@gmail.com)

    Dan juga saya diberi pilihan apakah saya ingin cek kertas dikirim kepada saya melalui jasa kurir, tetapi saya mengatakan kepada mereka untuk mentransfer uang ke rekening bank saya, karena saya berjanji bahwa saya akan membagikan kabar baik sehingga orang bisa mendapatkan pinjaman mudah tanpa stres atau penundaan.

    Yakin dan yakin bahwa ini asli karena saya memiliki semua bukti pemrosesan pinjaman ini termasuk kartu ID, dokumen perjanjian pinjaman, dan semua dokumen. Saya sangat mempercayai Madam ESTHER PATRICK dengan penghargaan dan kepercayaan perusahaan yang sepenuh hati karena dia benar-benar telah membantu hidup saya membayar proyek saya. Anda sangat beruntung memiliki kesempatan untuk membaca kesaksian ini hari ini. Jadi, jika Anda membutuhkan pinjaman, silakan hubungi Madam melalui email: (estherpatrick83@gmail.com)

    Anda juga dapat menghubungi saya melalui email saya di (siskawibowo71@gmail.com) jika Anda merasa kesulitan atau menginginkan prosedur untuk mendapatkan pinjaman

    Sekarang, yang saya lakukan adalah mencoba untuk memenuhi pembayaran pinjaman bulanan yang saya kirim langsung ke rekening bulanan Nyonya seperti yang diarahkan. Tuhan akan memberkati Nyonya ESTHER PATRICK untuk Segalanya. Saya bersyukur

    ReplyDelete
  11. Salam kepada semua warga negara Indonesia, nama saya Yeyes Ristintares tolong, saya ingin membagikan kesaksian hidup saya di sini di platform ini agar semua warga negara Indonesia berhati-hati dengan pemberi pinjaman di internet, Allah benar-benar mendukung saya melalui kebaikan Ibu Ny. Helen Wilson. Setelah beberapa periode mencoba untuk mendapatkan pinjaman dari lembaga keuangan, dan ditolak, jadi saya memutuskan untuk mendaftar melalui pinjaman online tetapi saya ditipu dan saya kehilangan lebih dari 32 juta Rupiah dengan pemberi pinjaman yang berbeda setelah membayar beberapa biaya dan tidak mendapatkan pinjaman. Saya menjadi sangat putus asa dalam mendapatkan pinjaman, jadi saya berdiskusi dengan seorang teman saya yang kemudian memperkenalkan saya kepada Ny. Helen Wilson, pemberi pinjaman di perusahaan, jadi teman saya meminta saya untuk melamar dari ibu Helen, jadi saya memanggil keberanian dan menghubungi Ibu Helen.

    Saya mengajukan pinjaman 900 juta dengan tingkat bunga 2%, sehingga pinjaman itu disetujui tanpa tekanan dan semua pengaturan dibuat pada transfer kredit, karena fakta bahwa itu tidak memerlukan jaminan dan jaminan untuk pinjaman transfer saya hanya diberitahu untuk mendapatkan sertifikat perjanjian lisensi aplikasi mereka untuk mentransfer kredit saya dan dalam waktu kurang dari 48 jam uang pinjaman telah disetorkan ke rekening bank saya.

    Saya pikir itu lelucon sampai saya menerima telepon dari bank saya bahwa akun saya dikreditkan dengan jumlah 900 juta. Saya sangat senang bahwa Allah akhirnya menjawab doa saya dengan memesan pinjaman saya dengan pinjaman asli saya, yang memberi saya keinginan hati saya. mereka juga memiliki tim ahli yang akan memberi tahu Anda tentang jenis bisnis yang ingin Anda investasikan dan cara menginvestasikan uang Anda, sehingga Anda tidak akan pernah bangkrut lagi dalam hidup Anda. Semoga ALLAH memberkati Ny. Helen Wilson untuk membuat hidup saya mudah, jadi saya menyarankan siapa pun yang tertarik mendapatkan pinjaman untuk menghubungi Ny. Helen melalui email: (helenwilson719@gmail.com) untuk Anda pinjaman

    Ada perusahaan palsu lain yang menggunakan kesaksian saya secara online untuk mencapai keinginan egois mereka, saya satu-satunya dengan kesaksian yang benar ini, harap berhati-hati terhadap orang-orang ini. Akhirnya saya ingin berterima kasih kepada Anda semua karena telah meluangkan waktu untuk membaca kesaksian sejati hidup saya tentang kesuksesan saya dan saya berdoa Allah akan melakukan kehendak-Nya dalam hidup Anda. Sekali lagi nama saya Yeyes Ristintares, Anda dapat menghubungi saya untuk informasi lebih lanjut melalui email saya: yristintares@gmail.com

    ReplyDelete
  12. Salam Semua.
    Saya Edi Sugiarto dari Yogyakarta, Allah telah dikaruniai dua orang anak dan Istri tercinta Linda Fitriawati, saya ingin membagikan kesaksian saya karena ALLAH mencintai saya. Setahun yang lalu saya sangat membutuhkan uang jadi saya berpikir untuk mengambil pinjaman. Kemudian saya bertemu seseorang, orang yang salah mengaku sebagai pemberi pinjaman, dan tidak tahu bahwa itu semua adalah penipuan. Saya ditipu seharga 27 juta Rupiah, dan mereka menolak untuk mentransfer pinjaman saya kepada saya, mereka juga berhenti mengirimi saya email sejak itu. Saya menjadi bingung, seluruh hidup saya hilang. Istri saya jatuh sakit dan ada tagihan rumah sakit yang harus dibayar jutaan, yang saya pikirkan saat ini hanya bunuh diri, teman saya bernama Santoso datang menemui saya pada hari yang naas itu, dia juga menjadi korban penipuan, dia memberi tahu saya tentang konferensi yang diselenggarakan oleh Wahyu Handoko untuk memberdayakan perempuan dan laki-laki yang ingin membuat kekayaan, dia meminta kakaknya untuk membantu saya mengurus istri dan anak-anak saya, jadi kami pergi untuk konferensi. Setelah semua motivasi berbicara, dia bertanya kepada kami pertanyaan "Apakah Anda Siap Untuk Apa yang Diperlukan Untuk Menjadi Kaya" dengan berani di jemaat kecil itu, saya berdiri dan berkata "YA" dan kami semua diminta untuk datang keesokan harinya dengan rencana bisnis .

    Kami pergi dan dia berbicara tentang bagaimana dia mendapatkan pinjamannya dan koneksinya melalui HELEN WILSON yang hebat, Pemberi Pinjaman online, segera saya takut, teman saya mendorong dan kami menghubungi Ibu Helen Wilson, seperti yang diarahkan oleh Wahyu Handoko dari konferensi. Saya dan teman saya mulai memproses sementara Pak Wahyu telah kembali, beberapa hari kemudian saya menerima telepon dari teman saya yang memberi tahu saya bahwa dia menerima peringatan dari bank, pinjamannya telah dilunasi, sudah terlambat sehingga saya tidak bisa pergi ke bank saya untuk konfirmasi, paginya pemberitahuan datang, akhirnya saya mendapat pinjaman sebesar 720 juta Rupiah dari Helen Wilson, setelah mengikuti proses hukum. kami diberi arahan untuk menyerahkan rencana bisnis kami dan meninggalkan uang di bank selama seminggu, kemudian Pak Handoko menelepon meminta kami untuk bertemu lagi yang kami patuhi, kami tiba di tempat itu dan melihat dampak orang asing terhadap perdagangan dan investasi, kami diberi kuliah dan kontak untuk mulai berinvestasi, dalam enam bulan melalui koneksi ibu Helen saya mulai mengimpor dan hari ini saya dan istri saya telah mendirikan dua perusahaan besar.

    Saya ingin Anda semua tahu bahwa satu-satunya pemberi pinjaman sejati yang saya saksikan adalah Ms. HELEN WILSON, hubungi dia hari ini dan Anda akan mendapatkan perubahan positif dalam hidup Anda, ini email helenwilson719@gmail.com. Anda dapat menghubungi saya di email saya sugiartoe385@gmail.com, untuk konfirmasi. Perhatikan, ada banyak pemberi pinjaman palsu online untuk menipu Anda, merobek Anda dari uang hasil jerih payah Anda, harus dari mereka pergi sejauh menyiapkan situs web pribadi mereka hanya untuk menipu Anda, pinjaman yang mengarahkan Anda untuk mengunjungi situs web palsu, mereka semua penipu .

    Jadi hubungi perusahaan induk Helen sekarang dan pinjaman Anda akan ditransfer kepada Anda saat Anda mengikuti proses hukum, sekali lagi ini adalah emailnya (helenwilson719@gmail.com) . ALLAH melihat hatiku dan dia tahu aku mengatakan yang sebenarnya dan tidak ada yang lain selain kebenaran.

    ReplyDelete